Neman Lalata: Majalisa Ta yi Watsi da Bukatar Natasha kan Zargin Akpabio
- Kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa ya yi watsi da bukatar watsa shari’ar Natasha Akpoti-Uduaghan kai tsaye a talabijin
- Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce majalisa na so a mayar da hankali kan batun ba tare da wata hayaniya ba
- Sai dai duk da haka, kwamitin ya tabbatar da cewa za a bai wa Sanata Akpoti-Uduaghan damar kare kanta tare da yin adalci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kwamitin ladabtarwa na ‘yan Majalisar Dattawa ya bayyana cewa ba za a watsa shari’ar da ke tsakanin Natasha Akpoti-Uduaghan da Godswill Akpabio, kai tsaye a talabijin ba.
Sanata Akpoti-Uduaghan ta bukaci a watsa zaman kwamitin kai tsaye domin a bai wa ‘yan Najeriya damar ganin yadda za a gudanar da shari’ar.

Asali: Twitter
Punch ta wallafa cewa shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a ranar Laraba, 5 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin kin amincewa da watsa zaman
Sanata Imasuen ya bayyana cewa kwamitin ya dauki wannan mataki ne domin guje wa duk wani abu da zai iya karkatar da hankali daga batun da ke gaban su.
Neda Imasuen ya ce:
“Muna son tabbatar da cewa ba za a mayar da wannan shari’a tamkar wata rigima ta kafafen yada labarai ba.
"Wannan al’amari ne na cikin Majalisar Dattawa, kuma ba mu son ya zama abin hayaniya.”
Sanatan ya kuma bayyana cewa dakin taron kwamitin ba zai iya daukar jama’a da yawa ba, domin kuwa akwai kimanin mambobi 23 ko 24 a kwamitin.
Ya kara da cewa a shirye suke su saurari duk wani korafi da Akpoti-Uduaghan za ta gabatar, tare da tabbatar da adalci.
Kwamitin majalisa ya ba da tabbacin adalci
Shugaban kwamitin ya tabbatar da cewa za a ba da cikakken adalci ga Sanata Akpoti-Uduaghan, tare da kare hakkokinta kamar sauran sanatoci.
Sanatan ya ce:
“Sanata Natasha tana da dukkan hakkoki kamar sauran sanatoci, kuma za a ba ta damar kare kanta.
"A matsayina na shugaban kwamitin, zan tabbatar da cewa an yi mata adalci. Ita abokiyar aikita ce, kuma ba wanda zai tauye mata ‘yanci.”
Sanatan ya kuma bayyana cewa ba za a bari a takurawa Akpoti-Uduaghan ko a hana ta damar bayyana matsayinta.

Asali: Facebook
Sanata Imasuen ya ki magana kan zargin
A lokacin da aka tambaye shi game da zargin cin zarafi da ake cewa an yi a Majalisar Dattawa, Imasuen ya ce ba zai iya yin magana kan batun ba domin tuni ana shari’a a kotu.
Leadership ta wallafa cewa Sanatan ya ce:
“Maganar cin zarafi a Majalisar Dattawa tuni ta shiga kotu, don haka ba zan iya yin tsokaci a kai ba. A matsayina na lauya, dole ne in mutunta doka.”
An bukaci Akpabio ya sauka a mukaminsa
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar mata ta bukaci shugaban majalisar dattawa ya ajiye mukaminsa kan zargin da ake masa.
Kungiyar matan ta ce hakan ne kawai zai ba da damar yin cikakken bincike da tabbatar da adalci ga Natasha Akpoti a majalisar dattawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng