Bayan Tsawon Shekaru da Tsige Shi, Gwamna Ya Mayar da Sarki kan Sarauta
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya dawo da sarkin Eruwa, Prince Adebayo Adegbola kan sarauta bayan shekaru sama da biyar da tsige shi
- An tattaro cewa tun farko Mai martaba Adegbola ya hau kan sarautar Eleruwa na Eruwa a 1998 amma rikicin da ya biyo ya jawo tsige shi a 2019
- Kwamishinan yaɗa labarai na Oyo ya ce bayan shafe shekaru babu basarake a masarautar, Makinde ya yanke shawarar dawo da Adegbola
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sake naɗa Prince Adebayo Adegbola a matsayin sabon Sarkin Eruwa watau Eleruwa na Eruwa da ke a ƙaramar hukumar Ibarapa ta Gabas.
Wannan naɗin ya biyo bayan shari’ar da aka kammala kwanan nan wacce ta tabbatar da cewa har yanzu ba a naɗa sarki ba tun bayan tsige Adegbola daga sarauta a 2019.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an naɗa Adegbola karon farko a matsayin sarkin Eruwa tun a shekarar 1998.
Yadda aka tsige sarkin Eruwa a kotu
Amma bayan shari’o’i da yawa da wasu ’yan masarautar suka shigar, Kotun Koli ta soke naɗinsa a ranar 29 ga Nuwamba, 2019.
Kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta ce ta gamsu da bayanin masu ƙara cewa an tafka rashin adalci da karya doka a hanyoyin da aka bi wajen naɗin basaraken.
Sai dai a sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kai na Oyo, Dotun Oyelade, ya fitar, ya bayyana cewa Gwamna Makinde ya amince da mayar da Adegbola kan sarauta.
Gwamna ya mayar da sarki kan sarauta
A cewarsa, hukuncin da babbar kotun jihar Oyo ta yanke a ranar 22 ga Oktoba, 2024, shi ne maƙasudin da gwamnati ta yanke shawarar mayar da Adegbola kan kujerarsa.
Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, Hon. Ademola Ojo, ya bayyana cewa bisa doka, iyalan Laribikusi ne ke da damar naɗa sabon sarki.
Amma bayan da suka kasa gabatar da sunayen masu takara a cikin wa’adin da doka ta tanada, an ba wa iyalan Akalako damar gabatar da ’yan takara.
A ƙarshe, masu zaben sarki sun amince da Prince Adebayo Adegbola a matsayin sabon Eleruwa.
Gwamna Makinde ya kafa tarihi a Oyo
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnatin Seyi Makinde ta naɗa sarakuna 11 da Baales 40 a cikin shekaru masu yawa, wanda hakan ya kafa tarihi a tsarin sarautar Yarbawa.
Ya yi kira ga al’ummar yankin masarautar Eruwa da su rungumi sabon sarki tare da mara masa baya domin haɗin kai da ci gaban masarautar.
A cewarsa, sabon Eleruwa zai yi aiki tukuru don kawo zaman lafiya da cigaba ga mutanensa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Gwamnatin Oyo ta musanta rasuwar Olubadan
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Oyo karkashin Gwamna Seyi Makinde ta karyata rahotannin da ke cewa Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu.
Wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewa basaraken ya rasu yana da shekaru 89, amma gwamnatin Makinde ta ce babu ƙanshin gaskiya a labarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


