Natasha: An Hura Wutar Sauke Akpabio, Barau Zai Iya Zama Shugaban Majalisa
- Kungiyar mata ta bukaci Godswill Akpabio ya sauka daga mukaminsa, a binciki zargin da Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi Godswill Akpabio da yunkurin yin lalata da ita yayin wata tattaunawa da suka yi
- Baya ga haka, kungiyar matan ta bukaci majalisa ta tabbatar da adalci da kare hakkin mata a harkar siyasa da sauransu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wata kungiyar kare hakkin mata ta VIEW ta bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da ya sauka daga mukaminsa domin gudanar da bincike a kansa.
Kungiyar ta yi magana ne kan zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi a kansa na yunkurin lalata da ita.

Asali: Twitter
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa a ranar 28 ga watan Fabrairu, Sanata Natasha, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta zargi Akpabio da yunkurin yin lalata da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar kungiyar, majalisa na da nauyin tabbatar da adalci da kare hakkokin mata daga duk wani nau’i na cin zarafi ko barazana a harkokin siyasa.
Mata sun bukaci a binciki Akpabio
A wata sanarwa da kungiyar VIEW ta fitar a ranar Talata, ta ce dole ne majalisa ta dauki matakin da ya dace domin tabbatar da cewa shugabanni ba su da iko na musguna wa mata.
Kungiyar ta ce:
"Idan aka yi la’akari da girman wannan zargi, yana zama wajibi a kan Shugaban Majalisar Dattawa ya sauka daga mukaminsa domin gudanar da bincike mai zaman kansa,"
Kungiyar ta bukaci a gudanar da bincike kan irin wadannan zarge-zarge da ake yi wa Akpabio, tare da cewa ba wannan ne karo na farko da ake yin irin wadannan zarge-zarge a kansa ba.
Tsarin mulkin Najeriya ya nuna cewa idan Sanata Akpabio ya sauka ko aka sauke shi, mataimakinsa, Barau Jibrin ne zai rike jagorancin majalisar.
Kungiyar VIEW ta ce kar a yi rufa-rufa
Kungiyar ta jaddada cewa kada a rufe wannan batu domin kare mutuncin wani mutum daya, tare da cewa dole a kare martabar mata ‘yan siyasa.
Bayanin kungiyar ya nuna cewa:
"Ba za a bar shari’a da adalci su zama tamkar kare mutum daya ba. Dole ne majalisa ta dauki matakin da zai tabbatar da cewa shugabanni ba su da kariya daga bincike,"
Kungiyar ta kara da cewa idan ba a dauki matakin da ya dace ba, hakan zai kara rage wa jama’a yarda da majalisa, tare da kara mayar da Najeriya inda masu mulki ke cin karensu ba babbaka.

Asali: Facebook
VIEW ta bukaci kare 'yancin mata a majalisa
A cewar kungiyar, duk wani yunkurin dakile Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ko rage kimar zargin da ta yi, tamkar take hakki ne ga daukacin ‘yan Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa idan aka bar irin wannan cin zarafi ya wanzu, hakan zai kara rage yawan mata masu shiga siyasa da kuma hana su fadin ra’ayinsu cikin ‘yanci.

Kara karanta wannan
Natasha: 'Yan siyasar Arewa sun huro wuta, suna so shugaban majalisa ya yi murabus
Natasha: An bukaci Akpabio ya yi murabus
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan siyasa daga Arewacin Najeriya sun bukaci shugaban majalisar dattawa ya sauka domin binciken zargin lalata da aka yi masa.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau na cikin wadanda suka bukaci Godswill Akpabio ya sauka a dalilin zargin da Natasha ta yi masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng