Ramadan: Gwamnatin Sokoto Ta Fadada Shirin Ciyarwa, Ta Fadi Wadanda Za Su Amfana
- Gwamnatin jihar Sokoto ta faɗaɗa shirin ciyarwa da take yi a watan azumin Ramadan na wannan shekarar
- Mai girma Gwamna Ahmed Aliyu ya raba N1.355bn don faɗaɗa shirin zuwa gundumomi 244 na faɗin jihar
- Gwamnan ya tabbatar da aniyarsa ta ganin cewa ya tallafawa nakasassu da marasa galihu a lokacin azumi
- Ya jawo hankalin waɗanda za su kula da kuɗin da su sanya tsoron Allah a zukatansu domin akwai ranar bayani
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya faɗaɗa shirin ciyarwa na watan Ramadan.
Gwamna Ahmed Aliyu ya raba N1.355bn don tallafawa cibiyoyin ciyarwa na azumin Ramadan a fadin jihar Sokoto.

Source: Twitter
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a gidan gwamnatin Sokoto a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Tribune.
Za a raba N1.355bn a Sokoto
A cewar gwamnan, za a raba kuɗin ne ga gundumomi 244 a cikin kananan hukumomi 23 da kuma cibiyoyin ciyarwa 27 da ke kula da masu nakasa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Gwamna Ahmed Aliyu ya tabbatar da aniyarsa ta tallafawa mabuƙata da marasa galihu a jihar.
Ya tuna cewa shirin ciyarwa a azumin Ramadan, wanda tsohon Gwamna Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya fara, an yi watsi da shi a zamanin gwamnatin da ta gabata, amma yanzu an farfaɗo da shi tare da faɗaɗa shi.
"Kuna iya tunawa cewa a makon da ya gabata, mun ƙaddamar da kwamitin ciyarwa na azumin Ramadan na jiha kuma mun fara raba kayan abinci ga cibiyoyin ciyarwa 150 a cikin birnin Sokoto.
"A yau, muna faɗaɗa wannan shirin zuwa ga dukkan gundumomi 244 da kuma masu nakasa a jihar."
- Gwamna Ahmed Aliyu
A cikin wannan shiri, kowace gunduma daga cikin guda 244 za ta karɓi N5m, haka kuma za a bai wa kowace cibiya daga cikin guda 27 na masu nakasa N5m domin samar da abinci da muhimman kayayyakin buɗa baki.
Gwamna Ahmed Aliyu ya yi gargaɗi

Kara karanta wannan
"Ɗan takara 1 tal gare mu," Sanatan APC ya hango wanda zai ci gaba da mulkin Najeriya a 2027
Gwamna Ahmed Aliyu ya gargaɗi masu kula da kuɗaɗen da su yi adalci tare da sanya tsoron Allah a zukatansu.
"Dole ne ku sanya tsoron Allah a duk abin da kuke yi, kuma ku tuna cewa wata rana za mu bayar da bayani a gaban Mahaliccinmu."
- Gwamna Ahmed Aliyu
Har ila yau, ya bukaci waɗanda za su amfana da shirin su kasance masu bin doka, tare da ba da haɗin kai yayin rabon abinci domin tabbatar da cewa ba a samu cikas ba.
Gwamnatin Kano ta ware N8bn don ciyarwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Ƙabir Yusuf ta shirya gudanar da shirin ciyarwa a watan azumin Ramadan.
Gwamnatin ta ware N8bn domin gudanar da shirin wanda mabuƙata da marasa galihu za su amfana da shi a lokacin azumi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
