Bayan Nada Shugaban NYSC, Tinubu Ya Sake Yin Muhimmin Nadi a Gwamnatinsa

Bayan Nada Shugaban NYSC, Tinubu Ya Sake Yin Muhimmin Nadi a Gwamnatinsa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabon Akanta Janar na Tarayya (AGF) da zai kula da sha'anin baitul mali
  • An amince da naɗin Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya a ranar Talata, 4 ga watan Maris 2025
  • Naɗin Shamseldeen zai fara aiki ne daga ranar 7 ga watan Maris, lokacin da Akanta Janar ta yanzu, Oluwatoyin Madein za ta yi ritaya
  • Tinubu ya taya Ogunjimi murna kan sabon muƙamin da ya samu, ya buƙace shi da ya yi aiki tuƙuru wajen sauke nauyin da aka ɗora masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon Akanta Janar na tarayya (AGF).

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na tarayya (AGF).

Kara karanta wannan

Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu ya yamutsa siyasar Kano a wurin buɗa bakin azumi

Tinubu ya nada sabon Akanta Janar na Tarayya
Shugaba Tinubu ya nada Akanta Janar na Tarayya Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai taimakawa Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, wacce Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Akanta Janar

Naɗin Shamseldeen Babatunde Ogunjimi, wanda aka amince da shi a yau, zai fara aiki daga ranar 7 ga watan Maris, 2025.

A wannan ranar ne mai riƙe da muƙamin a halin yanzu, Oluwatoyin Madein, za ta yi ritaya daga bakin aiki.

An fara bayyana shi a matsayin magajin Madein tun a watan Disamba na shekarar 2024 da ta gabata.

Daga baya wani kwamitin da aka kafa ya zaɓe shi domin riƙe muƙamin bayan an kammala tantance shi.

Kwamitin ya aiwatar da tsarin zaɓen ne ta hanyar matakai uku, gwaji ta hanyar rubutu, gwajin ƙwarewa a fannin fasahar ICT, da kuma tattaunawa ta baki.

"Tsarin zaɓen ya nuna irin jajircewar shugaba Tinubu wajen tabbatar da gaskiya, ƙwarewa, da cancanta a muhimman muƙaman hukumomin gwamnati."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka

"Shugaba Tinubu ya taya Ogunjimi murna bisa naɗin da aka yi masa, tare da bukatarsa da ya gudanar da aikinsa da gaskiya, ƙwarewa, da cikakkiyar sadaukarwa wajen hidimtawa Najeriya."

- Bayo Onanuga

Wane ne Shamseldeen Babatunde Ogunjimi?

Shamseldeen Ogunjimi ya kammala karatunsa daga jami’ar Najeriya, Nsukka, a shekarar 1990 da digiri na farko a fannin lissafin kuɗi.

Haka kuma, ya samu digiri na biyu a fannin lissafin kuɗi daga jami’ar Legas.

Ogunjimi mamba ne na cibiyar ƙwararrun masu lissafin kuɗi ta Najeriya da kuma cibiyar ƙwararrun masu karɓar haraji ta Najeriya.

Tinubu ya naɗa shugaban NYSC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC).

Shugaba Tinubu ya naɗa Birgediya-Janar Kunle Nafi'u a matsayin wanda zai ci gaba da jan ragamar hukumar NYSC.

Birgediya-Janar Kunle Nafi'u wanda ɗan asalin jihar Osun ne, ya karɓi ragamar shugabancin hukumar daga hannun Birgediya-Janar Yusha'u Ahmed.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng