Gwamnati Ta Haramta Duka a Makarantu, Ta Kawo Hanyar Hukunta Dalibai

Gwamnati Ta Haramta Duka a Makarantu, Ta Kawo Hanyar Hukunta Dalibai

  • Gwamnatin jihar Legas ƙarƙashin jagorancin Babajide Sanwo-Olu ta yi magana kan batun amfani da duka domin hukunta ɗalibai a makarantu
  • Kwamishinan ilmin firamare da sakandare na jihar, Jami'u Alli-Balogun ya tabbatar da cewa gwamnatin ta hana dukan ɗalibai a makarantu
  • A maimakon dukan, kwamishinan ya bayyana a yanzu an koma amfani da hanyar ba ɗalibai shawarwari idan suka yi laifi domin su gyara
  • Kamar yadda Jami'u Alli-Balogun ya fada, ba a hana amfani da sanya ɗalibai kwashe shara, yanke ciyawa ko durƙusawa ba idan suka yi laifi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Gwamnatin jihar Legas ta sake jaddada haramcin hukuncin duka a makarantu na gwamnati.

Gwamnatin ta jaddada cewa ba da shawarwari ya fi inganci fiye da amfani da duka wajen ladabtar da ɗalibai a makarantu.

Gwamnatin Legas ta haramta duka a makarantu
Gwamnatin Legas ta haramta dukan dalibai a makarantu Hoto: @Followlasg
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce kwamishinan ilmin firamare da sakandare na jihar, Jamiu Alli-Balogun, ya tabbatar da hakan wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya fusata, ya nemi a binciki rushe shagunan talakawa 500 a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Legas ta haramta dukan ɗalibai

Ya jaddada cewa har yanzu an haramta dukan dalibai saboda rashin ɗa’a da wasu laifuka don hana samun raunuka, suma ko ma mutuwa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

“Akwai wata doka a nan Legas da wasu sassan ƙasar nan da ke hana malamai dukan ɗalibai a matsayin hukunci.”
“Madadin duka, mun ɗauki ba ba shawarwari a matsayin hanyar gyara tarbiyya."

- Jami'u Alli-Balogun

Wace hanya za a bi wajen hukunta ɗalibai?

Yayin da yake goyon bayan ladabtarwa ba tare da duka ba, kwamishinan ya bayyana cewa ana iya amfani da ƙananan hukunci kamar durƙusawa, kwashe shara, ko yanke ciyawa a harabar makaranta a madadin duka.

Ya bayyana waɗannan hanyoyin a matsayin wata dabara mai kyau da ke nufin gyara halayen ɗalibai tare da zaburar da su wajen yin abin da ya dace.

“Manufar ita ce a fahimtar da ɗalibi dalilan da ya sa bai kamata ya aikata rashin ɗa’a ba. Shawarwarin na da nufin gyara ne kawai.”

Kara karanta wannan

Ramadan: Hukumar Hisbah ta ci gaba da aikin Allah cikin watan Azumi a Kano

- Jami'u Alli-Balogun

An ba iyayen yara shawara

Kwamishinan ya danganta yawancin matsalolin rashin ɗa’a da dalibai ke yi da rashin samun kyakkyawan tarbiyya daga iyaye, yana mai kira ga iyaye da su fi sa ido kan rayuwar ƴaƴansu.

Ya kuma bayyana cewa tun bayan haramta duka, ladabin ɗalibai ya inganta sosai, inda suka fi kula da halayensu da kuma illolin da ka iya biyo baya.

Gwamnatin jihar Legas ta haramta hukuncin duka a makarantu na gwamnati da masu zaman kansu tun a shekarar 2022.

Gwamnoni sun tabbatar da kulle makarantu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatocin jihohin Arewa da suka kulle makarantu saboda azumin Ramadan, sun yi wa ƙungiyar CAN martani.

Gwamnatocin sun bayyana cewa ba gudu ba ja da baya kan hutun da aka ba ɗaliban makarantun firamare da sakandare saboda azumin watan Ramadan.

Hakan na zuwa ne bayan ƙungiyar CAN ta yi barazanar zuwa kotu saboda rufe makarantun da aka yi a jihohin Bauchi, Kano, Katsina da Kebbi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng