Ramadan: Bayan Rufe Makarantu, Gwamna Ya Rage Lokutan Aiki saboda Azumi

Ramadan: Bayan Rufe Makarantu, Gwamna Ya Rage Lokutan Aiki saboda Azumi

  • Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma’aikatan gwamnati lokutan aiki don saukaka musu azumin watan Ramadan
  • Ma’aikata za su rika fara aiki da karfe 9:00 na safe su tashi da karfe 3:00 na yamma daga Litinin zuwa Alhamis
  • Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne don bai wa ma’aikata damar gudanar da ibada cikin sauki yayin azumi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rage wa ma’aikatan gwamnati lokutan aiki domin saukaka musu yayin azumin watan Ramadan.

Sanarwar hakan ta fito daga shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya bayyana cewa rage lokutan aiki zai fara aiki nan take.

Jigawa
Gwamnatin Jigawa ta rage lokutan aiki saboda azumi. Hoto: Garba Muhammad
Asali: Facebook

A cewar Daily Trust, matakin wani yunkuri ne na Gwamna Umar Namadi domin bai wa ma’aikata damar shiryawa buda-baki da kuma gudanar da ayyukan ibada cikin sauki.

Kara karanta wannan

Azumi: 'Dan majalisar NNPP ya ware mutane 10,000 ya raba musu miliyoyin Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon tsarin aiki lokacin azumi a Jigawa

Gwamnatin Jigawa ta bayyana cewa daga yanzu, ma’aikatan gwamnati za su fara aiki da karfe 9:00 na safe su kuma tashi da karfe 3:00 na yamma daga Litinin zuwa Alhamis.

A ranar Juma’a kuwa, ma’aikatan za su shiga ofis da misalin karfe 9:00 na safe su tashi da karfe 1:00 na rana, domin su samu damar shiryawa sallar Juma’a da sauran ayyukan ibada.

Punch ta wallafa cewa matakin rage wa ma’aikata lokacin aiki wani kokari ne na gwamnatin jihar don ba su damar gudanar da ibada cikin sauki a wannan wata mai alfarma.

Gwamnati ta bukaci ma'aikata su yi addu'a

Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar ya bayyana cewa gwamnatin Jigawa na fatan ma’aikata za su yi amfani da wannan dama don yin addu’a ga jihar da kasa baki daya.

"Fatanmu shi ne ma’aikatan jihar za su yi amfani da wannan wata domin yin addu’a ga zaman lafiya da albarka a Jigawa da Najeriya baki daya,"

Kara karanta wannan

Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan

- Alhaji Muhammad Kandira Dagaceri

Ya kara da cewa Ramadan wata ne na ibada da neman rahamar Allah, don haka gwamnatin jihar na fatan wannan sauki zai taimaka wajen karfafa ayyukan ibada a tsakanin ma’aikata.

Gwamna Namadi
Gwamna Nadami yayin raba tallafi a Jigawa. Hoto: Garba Muhammad
Asali: Facebook

Inganta walwalar ma'aikata a Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce rage lokutan aiki a watan Ramadan yana daya daga cikin kokarin da take yi na kyautata jin dadin ma’aikatan gwamnati.

A cewar sanarwar, Gwamna Umar Namadi na da kishin ma’aikata kuma yana kokarin samar da yanayi da zai ba su damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.

Gwamnatin ta bukaci ma’aikatan su yi amfani da lokacin domin yin aiki da gaskiya da rikon amana, tare da amfani da lokacin su yadda ya kamata.

Gwamnatoci sun yi martani ga CAN

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jihohin Kano, Bauchi da Kebbi sun ce ba za su sauya matsaya ba kan rufe makarantu a Ramadan.

Kara karanta wannan

NAHCON ta sanar da fara daukar ma'aikata domin aikin hajjin 2025

Hakan na zuwa ne bayan kungiyar Kiristoci ta CAN ta bukaci jihohin su bude makarantun da suka kulle da sunan hutun azumin bana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng