Boko Haram Ta Tsallaka, Ta Kai Harin Ramuwar Gayya a Neja, Ta Kashe Bayin Allah
- Mayakan Boko Haram sun kai wani mummunan hari da ake zaton na ramuwar gayya ne a ƙauyen Karaga da ke Jihar Neja
- Rahotanni sun bayyana cewa ana kyautata zaton harin na ramuwar gayya ne bayan jami'an tsaro sun yi wa kungiyar Boko Haram illa
- A watan Oktoba ne aka hallaka manyan dakarun Boko Haram guda biyar, ciki har da wani ƙwararre a harkar abubuwa masu fashewa
- A harin da ta kai a matsayin martani, kungiyar ta hallaka maza kacokan, yayin da ta bar mata da yara da ba su haura shekaru 12 ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger - Akalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da ake zargin ‘yan Boko Haram sun kai a wajen hakar zinariya da ke ƙauyen Karaga, a jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa wurin hakar ma'adinan yana kusa da mafakar kungiyar a dajin Alawa da ke yankin Shiroro a jihar.

Asali: Twitter
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa majiya daga yankin da kuma jami’an tsaro sun tabbatar da cewa harin ya faru ne a ranar 27 ga Fabrairu, 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa mayakan sun kai farmaki kan masu hakar ma'adinai da suka fito daga garin Bassa da wasu ƙauyuka da ke kewaye da shi.
Boko Haram ta addabi mazauna Neja
News Central TV ta wallafa cewa yankin Bassa, wanda a baya Boko Haram ta addaba da hare-hare, ya fara samun zaman lafiya bayan an tura sojoji yankin a 2024.
Sai dai tun bayan wani artabu da ya faru a watan Oktoba, inda Boko Haram ta yi asarar dakarunta, kungiyar ta ƙara tsananta kai hare-haren sari-ka-noke.

Asali: Twitter
Sun fara dasa abubuwan fashewa da kai hare-hare a ƙauyukan da ba su da isasshen kariya daga jami’an tsaro.
Tsofaffin 'yan ƙungiyar sun tabbatar da cewa a artabun watan Oktoba, an kashe mutum biyar daga ɓangaren Boko Haram, har da wani kwararren masanin fashewa mai suna Baba Adamu.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa harin da aka kai a ranar 27 ga Fabrairu na iya zama ramuwar gayya kan asarar da kungiyar ta yi.
Boko Haram ta farmaki ma’aikata
Maharan sun kai farmaki ne da tsakar dare, inda suka kashe duk manyan maza da suka samu a wurin, tare da barin mata da ƙananan yara masu shekaru 10 zuwa 12.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kashe wasu mafarauta biyu da ke barci a wurin, wanda ya kawo yawan mutanen da aka kashe zuwa 11.
Wani mazaunin Bassa mai suna Ibrahim Tanko ya tabbatar da kisan, tare da bayyana cewa an kai wasu biyu asibitin Minna domin ceto rayuwarsu.
Zuwa yanzu, an tabbatar da binne mutum bakwai a wurin da aka kai harin, yayin da aka binne sauran mutanen a garin Bassa.
'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun sace Farfesa Abubakar Eljuma, babban malami a Jami’ar Sojojin Najeriya da ke Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace Farfesa Eljuma ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Maris, 2025, a kan titin Damaturu-Biu, kusa da garin Kamuya, wanda da ke fama da matsalar tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng