Gaskiya Ta Fito da Aka Yada Labarin Allah Ya Karbi Rayuwar Fitaccen Basarake

Gaskiya Ta Fito da Aka Yada Labarin Allah Ya Karbi Rayuwar Fitaccen Basarake

  • Gwamnatin Oyo ta mayar da martani kan jita-jitar da ake yaɗawa game da mutuwar Mai Martaba Olubadan a jihar
  • Gwamnatin ta karyata rade-radin cewa Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu, ta tabbatar da cewa yana nan lafiya
  • Wasu rahotanni sun ce Oba Olakulehin ya mutu yana da shekaru 89 wanda aka tabbatar cewa sam babu gaskiya a labarin
  • Mai magana da yawun Olubadan, Gbenga Ayoade, ya ce basaraken yana nan lafiya, ya kuma karyata cewa an fita da shi neman magani

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Gwamnatin Jihar Oyo ta karyata rahotannin da ke cewa Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu.

Gwamnayin jihar ta bayyana cewa basaraken yana nan lafiya ba kamar yadda ake yaɗawa ya mutu yana da shekaru 89 a duniya ba.

Kara karanta wannan

Ana binciken Natasha maimakon Akpabio duk da zargin shugaban majalisa da lalata

Gwamnatin Oyo ta fadi halin da Basarake Olubadan ke ciki
Gwamnatin jihar Oyo ta ƙaryata labarin mutuwar basarake, Olubadan. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Yadda aka yada labarin mutuwar Olubadan na Ibadan

A wata hira da jaridar Punch, kwamishinan al’adu na Oyo, Wasiu Olatunbosun, ya ce labarin kwata-kwata ba gaskiya ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewa basaraken ya rasu yana da shekaru 89 yayin da wasu ke cewa an fita da shi kasar waje domin neman magani.

Kwamishinan ya ce:

"Eh, Olubadan yana nan da rai kuma cikin koshin lafiya, na yi magana da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, Prince Olaseke Owolabi Olakulehin."
An gano gaskiya kan jita-jitar mutuwar basarake a Najeriya
Gwamnatin Oyo ta musanta labarin rasuwar basarake a Ibadan. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Fadar basaraken ta fadi halin da yake ciki

Hakazalika, mai magana da yawun Olubadan, Gbenga Ayoade, ya ce labarin karya ne, ya tabbatar da cewa basaraken yana nan cikin koshin lafiya.

Ya ce:

"Lokacin da na bar fada da misalin ƙarfe 8 na dare, babu wata matsala, Komai yana tafiya lafiya daga baya, sun tabbatar min cewa yana lafiya."
"Olubadan ma har ya gama cin amala, yana cikin koshin lafiya, Wannan jita-jita ce kawai, babu gaskiya a ciki."

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga wani hali da tsohuwar Minista ta rasu a Najeriya, ya tura sako

Ayoade ya kuma karyata jita-jitar cewa an fita da basaraken daga garin domin jinya, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Ya ce:

"Baba yana nan a Ibadan, ba a fita da shi ko ina ba, yana cikin koshin lafiya."

Oba Olakulehin ya karɓi sandar mulki daga Gwamna Seyi Makinde a ranar 12 ga Yuli, 2024, an ce ranar 5 ga Yuli, 2025, zai cika shekaru 90.

Ya gaji Oba Mahood Lekan Balogun, wanda ya rasu a ranar 14 ga Maris, 2024, yana da shekaru 81 a duniya.

Sarkin Hausawa a jihohin Kudu ya rasu

Kun ji cewa Allah ya yi wa Sarkin Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan ya shafe shekaru da dama kan karagar mulki.

Marigayin kafin rasuwarsa, shi ne ke riƙe da muƙamin Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudu.

An tabbatar cewa an yi jana'izarsa a ranar Lahadi 2 ga watan Maris, 2025 a gidansa da ke birnin Ibadan yayin da Sarakunan Hausawa da malaman addini suka fara zaman makoki a fadarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel