Shugaba Tinubu Ya Amince da Kafa Sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya, An Jero Sunayensu

Shugaba Tinubu Ya Amince da Kafa Sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya, An Jero Sunayensu

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i 11 na kudi a Najwriya domin bunkasa harkokin ilimi
  • Ministan Ilimi na Tarayya, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa (FEC) ranar Litinin
  • Ya ce gwamnati ta bai wa sababbin jami'o'in lasisin wucin gadi kuma za ta ido ta tabbatar sun cika sharuɗɗan hukumar NUC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da ƙirƙiro sababbin jami'o' 11 masu zaman kansu ma'ana na kudi a faɗin ƙasar nan.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ba sababbin jami'o'in na kudi lasisin wucin gadi domin su fara aiki a Najeriya.

Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya amince da kafa jami'o'in kudi 11 Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya amince da jami'o'i 11

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, gwamnatin Najeriya ta ba jami'o'in damar fara aiki ne a wani yunkuri na bunƙasa harkokin ilimi da faɗaɗa damar shiga jami'o'i.

Kara karanta wannan

Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu ya yamutsa siyasar Kano a wurin buɗa bakin azumi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Ilimi na Tarayya, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci taron FEC a Aso Villa yau Litinin, 3 ga watan Maris, 2025 daidai da 3 ga watan Ramadan, 1446H.

Jerim sunayen sababbin jami'o'in

1. New City University, Ayetoro – Jihar Ogun

2. University of Fortune, Igbotako – Jihar Ondo

3. Eranova University, Mabushi – Abuja, FCT

4. Minaret University, Ikirun – Jihar Osun

5. Abubakar Toyin University, Oke-Agba – Jihar Kwara

6. Southern Atlantic University, Uyo – Jihar Akwa Ibom

7. Lens University, Ilemona – Jihar Kwara

8. Monarch University, Iyesi-Ota – Jihar Ogun

9. Tonnie Iredia University of Communication, Benin City – Jihar Edo

10. Isaac Balami University of Aeronautics and Management, Lagos – Jihar Lagos

11. Kevin Eze University, Mgbowo – Jihar Enugu

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka

Kara yawan jami’o’i zai Inganta Ilimi

A cewar Ministan Ilimi, amincewa da wadannan jami’o’i abu ne mai matukar muhimmanci domin kara habaka damar samun ingantaccen ilimi a Najeriya.

Tunji Alausa ya kara da cewa:

"Shugaba Bola Tinubu na da burin ganin an inganta harkar ilimi a kasar nan. Wannan matakin zai taimaka wajen rage cunkoso a jami’o’in gwamnati da kuma samar da karin guraben karatu ga matasa."

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ci gaba da karfafa duk wani yunkuri na habaka ilimi.

Ta kuma sha alwashin tabbatar da cewa wadannan sababbin jami’o’i sun cika duk ka’idojin da hukumar kula da jami’o’i (NUC) ta gindaya, Tribune ta ruwaito.

Wannan mataki ya sa a yanzu Najeriya na da jami'o'i sama da 150 a faɗin jihohi 36 da Abuja kuma galibinsu na kudi ne.

Tinubu ya kirkiro jami'o'i 2 na tarayya

A wani labarin, kun ji cewa Mai girma Bola Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'in tarayya guda biyu a Najeriya domin bunkasa harkokin ilimi.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno, sun sace babban farfesa da fasinjoji

Jami’o’in da aka kafa sun hada da Jami’ar Fasaha da Kimiyyar Muhalli, Iyin Ekiti da Jami’ar Noma da Nazarin Ci Gaba, Iragbiji, Osun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262