Ramadan: Sanata Ya Share Hawaye ga Talakawa da Ya Raba Tirelar Abinci 496
- Sanata Abdulaziz Yari ya raba kayan abinci ga mabukata a fadin jihar Zamfara domin saukaka musu wahala a watan Ramadan
- Kayan abincin da suka hada da shinkafa, gero, masara da sukari za a rabawa jama'a a kananan hukumomi 14 da ke Zamfara
- Biyo bayan lamarin, jama’a sun nuna godiya ga Sanata Yari, tare da bukatar sauran ‘yan siyasa su yi koyi da shi wajen raba tallafi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Sanata Abdulaziz Yari Abubakar mai wakiltar yankin Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa, ya kaddamar da rabon abinci.
Rahotanni sun nuna cewa Sanata Abdulaziz Yari ya raba tirela 496 cike da kayan abinci ga mabukata a fadin jihar Zamfara.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an fara rabon ne a Kaura Namoda, inda Sanata Yari ya bukaci masu kula da rabon su yi aiki da gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Yari ya bayyana cewa an shirya rabon ne domin tallafawa jama'a yayin watan azumin Ramadan.
Rabon kayan abinci a kananan hukumomi 14
Sanata Yari ya bayyana cewa rabon kayan abincin zai gudana lokaci guda a dukkan kananan hukumomi 14 da ke jihar Zamfara.
Ya tabbatar da cewa an tsara rabon ne domin a tabbatar da cewa kowa ya ci gajiyar tallafin a mazabu 147 da ke fadin jihar.
Wakilin Sanata Yari, Dr Lawal M. Liman, ya tabbatar wa al'umma cewa rabon kayan zai kammala cikin kwanaki hudu.
“Mun tanadi wadannan kayayyakin ne domin rage radadin da jama’a ke fuskanta a cikin wannan lokaci mai albarka na Ramadan,”
- Abdulaziz Yari
Tsarin rabon kayan abincin Sanata Abdulaziz Yari
Rahoton Trust Radio ya nuna cewa Sanata Yari ya bayyana cewa kowanne mutum biyar za su raba buhu daya na shinkafa.

Kara karanta wannan
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace shugabannin APC a kan hanyarsu ta zuwa gidan Sanata
Haka kuma za a raba buhunan gero da masara ga al'umma, yayin da kowane mutum zai samu kilo 1 na sukari yayin rabon.
Sanatan ya bukaci wadanda ke kula da rabon su guji nuna son zuciya da kuma tabbatar da cewa kayan sun isa ga wadanda suka cancanta.
"Abinci ya isa ga mabukata ba tare da nuna bambanci ko rashin adalci ba,"
- Sanata Abdulaziz Yari
Jama'a sun yi godiya ga Sanata Yari
Bayan an fara rabon kayan abincin, jama'a sun nuna farin ciki da godiya ga Sanata Yari bisa wannan kyauta.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana cewa hakan zai taimaka musu sosai a cikin wannan wata mai alfarma.
Haka kuma, wasu daga cikin jama’a sun bukaci sauran sanatoci da ‘yan siyasa su bi sahun Yari wajen tallafa wa al’umma.

Asali: Twitter
Ana sa ran cewa tallafin zai isa ga wadanda suka dace domin rage musu radadin tsadar rayuwa a watan Ramadan.
Sanata Goje ya raba tallafi a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Danjuma Goje ya raba kayan tallafi da mutanen mazabarsa ta Gombe ta Tsakiya.
Sanata Danjuma Goje ya raba kekunan dinki da wasu kudi domin rage zaman kashe wando da samar da ayyukan yi ga mutanensa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng