Gwamna Zulum Ya Tuna da 'Yan Kasuwa, Ya Yi Musu Rangwame cikin Ramadan
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi wa ƴan kasuwan da ambaliyar ruwa da kuma gobara ta shafa rangwame
- Zulum ya amince da janyewa ƴan kasuwan biyan kuɗin haraje har na tsawon shekara biyu domin sauƙaƙa musu kan asarar da suka yi
- Ƴan kasuwan da za su ci wannan rangwamen, sun haɗa da ƴan kasuwa da gobara ta shafa a kasuwar Monday Market da ke birnin Maiduguri
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umar Zulum, ya amince da dakatar da karɓar haraji na tsawon shekaru biyu daga hannun ƴan kasuwa.
Gwamna Zulum ya janye harajin ne ga ƴan kasuwar da ambaliyar ruwa ta watan Satumban 2024 da gobarar kasuwar Maiduguri Monday Market suka shafa.

Source: Facebook
Shugaban hukumar karɓar haraji ta jihar Borno (BO-IRS), Farfesa Ibrahim Bello, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka sanya a shafin Facebook na gwamnatin Borno.
Meyasa Zulum ya janye haraji?
Farfesa Ibrahim Bello ya ce wannan mataki na da nufin farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma ragewa ƴan kasuwa biyan kuɗaɗe kan kasuwancinsu.
Ya bayyana cewa wannan rangwame yana cikin sauye-sauyen da gwamnatin jiha ke yi a tsarin karɓar haraji, domin sauƙaƙa kasuwanci da ƙarfafa ci gaban tattalin arziƙi.
Da wannan rangwamen harajin, Gwamna Zulum na fatan tallafawa ƴan kasuwa da iftila'i ya shafa, domin su sami damar farfaɗowa da zuba jari a kasuwancinsu ba tare da ƙarin nauyin biyan kuɗin haraji ba.
A cewar Farfesa Ibrahim Bello, jihar Borno ta samu ci gaba sosai wajen inganta tsarin haraji.
Ya jaddada cewa harajin da ake karɓa a halin yanzu ana amfani da shi ne wajen manyan ayyuka na ci gaba, kamar gina tituna da inganta muhalli a yankuna irin su Jiddari, Umarari, GRA, Bulumkutu, Chad Basin, da wasu muhimman wurare.
Wane amfani ƴan kasuwan za su samu?

Kara karanta wannan
Uba Sani ya fusata kan 'yan siyasar da ke siyasantar da rashin tsaro, ya fadi matakin dauka
Wannan dakatar da haraji zai ba da dama ga ƴan kasuwa su murmure daga asarar da suka yi tare da ci gaba da kasuwancinsu.
Rage musu nauyin biyan kuɗin harajin zai ƙarfafa harkokin cinikayya a cikin gida da kuma ƙara jawo hankalin masu zuba jari, wanda zai haɓaka tattalin arziƙin jihar.
Bugu da ƙari, wannan mataki zai ƙarfafa ƙarfin tattalin arziƙin jihar, ta yadda zai iya jurewa matsaloli ko ƙalubalen da ka iya tasowa a nan gaba.
Har ila yau, yayin da jihar ke ci gaba da ƙarfafa tsarin karɓar haraji, ana sa ran wannan shiri zai ƙarfafa al’umma wajen biyan haraji, wanda zai samar da tsari mai ɗorewa domin samar da kuɗaɗen shiga.
Zulum ya rage yawan tallafin abinci
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum, ta sanar da rage yawan tallafin abincin da take bayarwa.
Gwamna Zulum wanda ya rage tallafin da kaso 90%, ya ce za a yi hakan ne domin ƙarfafa gwiwar mutanen jihar kan su dogara da kansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
