"Abin a Yaba": Coci Ta Gwangwaje Al'ummar Musulmi da Kayan Azumin Ramadan
- Wata coci mai suna Christ Evangelical and Life Intercessory da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna ta raba hatsi ga al'ummar Musulmi
- Cocin ta raba hatsi ga al'ummar Musulmi mutum 1000 da makarantun Islamiyya domin azumin watan Ramadan wanda aka fara
- Babban faston cocin ya bayyana, Fasto Yohanna Buru, ya bayyana cewa sun kwashe fiye da shekara 19 suna gudanar da irin hakan a jihohi biyar na Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Cocin Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry, Sabon Tasha, da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, ta raba hatsi ga al'ummar Musulmi domin azumin watan Ramadan.
Cocin ta raba hatsi ga mutum 1,000 da kuma makarantun Islamiyya domin sauƙaƙa musu azumin Ramadan, duba da halin ƙuncin rayuwa da ake ciki a ƙasar.

Source: Original
Babban Faston cocin, Fasto Yohanna Buru, ya bayyana hakan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa cocin ta raba kayan azumi?
Faston ya bayyana cewa wannan kyauta na da nufin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiyan addinai a yankin.
"Muna maida alherin da Hajiya Ramatu Tijjani, wata mata Musulma, ke yi mana, wacce ke bayar da shinkafa, kuɗi, da sababbin kaya ga zawarawa da marayu na cocin a lokacin bikin Kirsimeti, sabuwar shekara da Easter."
A cewarsa, cocin ta shafe shekaru 19 tana rabon shinkafa, masara, da wasu kayan abinci ga Musulmai marasa ƙarfi a jihohi biyar na Arewacin Najeriya, domin su samu damar yin azumin kwanaki 30 da addu’o’in Ramadan cikin sauƙi.
"A bana, muna da niyyar taimakawa Musulmai marasa galihu fiye da 1,000. Mun sayi buhunan masara da gero 30 domin raba su, kuma za mu fara rabon daga yau."
- Fasto Yohanna Buru
Fasto ya yi kira ga masu hannu da shuni
Ya yi kira ga masu hali da su tallafawa mabuƙata, tare da yin gargaɗi ga ƴan kasuwa da su guji ƙarin farashin kayan abinci ba bisa ƙa’ida ba a lokacin Ramadan.
Faston ya ƙara da cewa, ya tara Fastoci da limamai 30 don gudanar da yaƙin neman sassauta farashin kayan abinci na tsawon kwana bakwai domin jawo hankalin ƴan kasuwa su rage tsadar kayan abinci.
Da yake karɓar tallafin, Malam Hassan Lawal, shugaban ƙungiyar masu nakasa a jihar, ya nuna godiyarsa ga cocin.
Haka kuma, Malam Tukur Zubairu, shugaban ƙungiyar makafi ta jihar Kaduna, ya yaba da irin gudunmawar da cocin ke bayarwa ga Musulmai a duk lokacin azumin Ramadan.
Ganduje ya taya Musulmi murnar shigowar Ramadan
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya taya al'ummar Musulmai murnar shigowar watan azumin Ramadan mai alfarma.
Ganduje ya buƙaci al'ummar Musulmi da su zage damtse wajen gudanar da ibada tare da taimakon masu ƙaramin ƙarfi a cikin watan Azumin.
Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su sanya Shugaba Bola Ahmed Tinubu a cikin addu'o'insu domin ya gudanar da manufofinsa na ci gaban ƙasa.
Asali: Legit.ng

