Abin Tausayi: Dalibar Jami'a Ta Mutu a Hannun Yan Bindiga duk da Biyan Miliyoyi a Zamfara

Abin Tausayi: Dalibar Jami'a Ta Mutu a Hannun Yan Bindiga duk da Biyan Miliyoyi a Zamfara

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa dalibar da yan bindiga suka sace watanni hudu baya ta riga mu gidan gaskiya duk da cika sharudan maharan da aka yi
  • Marigayiyar mai suna Zarah Abubakar Shehu, mai shekaru 21 tana karatu a Jami’ar Tarayya Gusau, ta mutu bayan an biya fansa na miliyan da babura
  • Masu garkuwa sun fara neman ₦35m daga bisani suka amince da ₦10m, amma bayan an biya, sun ƙi sakin ta, suna neman ƙarin kayayyaki daga iyayenta
  • Bayan an cika buƙatunsu, shugaban masu garkuwa ya gano cewa Zarah ta mutu, kuma an riga an binne ta kwanaki biyu kafin sanarwar da suka yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - An shiga jimami bayan mutuwar Zarah Abubakar Shehu, ɗaliba mai shekaru 21 daga Jami’ar Tarayya a Gusau da ke jihar Zamfara a hannun yan bindiga.

Kara karanta wannan

Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan

Yan bindiga sun sace dalibar ce watanni huɗu da suka gabata tare da ‘yan uwanta a ranar 3 ga watan Nuwambar 2024 da ta gabata.

Daliba ta rasa ranta a hannun yan bindiga bayan biyan kudin fansa
Dalibar Jami'a, Zarah Abubakar ta mutu a hannun yan bindiga duk da biyan miliyoyi a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan bindiga sun sace dalibai 4 a Zamfara

Rahoton Vanguard ya ce ‘yan bindiga sun kutsa gidansu Zarah a yankin Damba, Gusau inda suka yi garkuwa da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki a Paris Quarters da ke bayan jami’ar tarayya ta Dutsinma, inda suka sace dalibai hudu.

Majiyoyi sun nuna cewa ‘yan bindigar sun mamaye yankin da misalin karfe 2:20 na dare, inda suka sace daliban kafin jami'an tsaro su kai dauki.

Yawan satar dalibai musamman na manyan makarantu ya zama ruwan dare a jihar Zamfara da ma yankin Arewacin Najeriya gaba daya tun bayan fara ayyukan ta'addanci.

Dalibar da ke hannun yan bindiga fiye da watanni 4 ta mutu
Dalibar jami'a da aka sace a Zamfara ta mutu a hannun yan sanda. Hoto: @ZagazOlamakama, HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Yadda daliba ta mutu a hannun yan sanda

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun sace ɗaliban jami'a 4 a wasu jihohin Arewa

Yan bindigar sun fara neman kudin fansa kan ₦35m, amma daga bisani suka amince da ₦10m bayan tattaunawa.

Duk da an biya kuɗin, sun ƙi sakin ta inda suka buƙaci babura huɗu (Boza) da man inji kafin su sake su, cewar Daily Post.

Bayan an samar da buƙatun, aka sanar da shugabansu, sai dai ya kira mutanensa, suka ce Zarah ta riga ta mutu, kuma an binne ta kwanaki biyu kafin sanarwa.

Marigayiya Zarah, ita ce kaɗai ‘yar da mahaifiyarta ke da ita, ta shafe wata huɗu a hannun masu garkuwa kafin ajali ya risketa.

Yan bindiga sun sace shugabannin APC a Zamfara

A baya, kun ji cewa wasu yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da shugabannin APC biyar daga Kaura Namoda ta Kudu yayin da suke tafiya Mafara.

An ce lamarin ya faru ne ranar Asabar 1 ga Maris, 2025 a yankin da ke Zamfara a Arewacin Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Daga cikin wadanda aka sace akwai Yahaya Sani Dogon Kade, Shugaban Dan Isah Ward, da Bello Dealer, Shugaban Sakajiki Ward, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.