Uba Sani Ya Fusata kan 'Yan Siyasan da Ke Siyasantar da Rashin Tsaro, Ya Fadi Matakin Dauka
- Gwamnan jihar Kaduna ya nuna ɓacin ransa kan yadda ƴan siyasa ke siyasantar da matsalar rashin tsaro
- Malam Uba Sani ya gargaɗi ƴan siyasan da ke yin hakan da su shiga taitayinsu domin suna jefa rayuwar mutane cikin hatsari
- Gwamna Uba Sani ya nuna cewa shirin sulhu da ƴan bindiga da gwamnatinsa ta ɓullo da shi ya haifar da ɗa mai ido
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ja kunnen ƴan siyasa dangane da matsalar rashin tsaro.
Gwamna Uba Sani ya gargaɗi ƴan siyasa da ke siyasantar da batun tsaro a matsayin adawa da su daina yin hakan, saboda suna jefa rayuwar mutane cikin hatsari.

Source: Twitter
Gwamna Uba Sani wanda ya bayyana hakan a ƙarshen mako, ya yi alƙawarin ɗaukar mataki kan irin waɗannan ƴan siyasa da ke jin dadin taɓarɓarewar tsaro domin cimma burinsu na siyasa, cewar rahotpn jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uba Sani ya ja kunnen ƴan siyasa
Ya yi wannan jawabi ne a zauren Sir Kashim Ibrahim House yayin da ya karɓi mutane 58 da aka sace waɗanda jami’an tsaro suka ceto, sannan aka miƙa su ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
"Masu cin kasuwa da rashin tsaro ba za su ji daɗin sakin waɗannan bayin Allah ba domin suna cin moriyar rashin tsaro."
“A matsayina na gwamnan da aka zaɓa, na yi rantsuwa zan kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kaduna, kuma muna iyakar ƙoƙarinmu wajen sauke wannan nauyin."
"Ta hanyar shirin sulhu da muka ɓullo da shi, wanda ya maida hankali kan amfani da hanyoyin da ba na yaƙi ba, yankin Birnin Gwari da aka fi sani da wurin da ba a iya shiga, yanzu ya samu zaman lafiya."
"Ƴan bindiga sun ajiye makamansu, kasuwanni da suka rufe fiye da shekara 10 an buɗe su, kuma harkokin kasuwanci sun fara bunkasa a Birnin Gwari da wasu sassan ƙaramar hukumar Giwa da rikici ya ɗaiɗaita."

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun hallaka 'yan sa kai a Kebbi
- Gwamna Uba Sani
Uba Sani ya ba jama'a tabbaci
Gwamna Uba Sani ya yi alƙawarin cewa mutanen Kauru, Kajuru da wasu sassan Kachia da ke fama da hare-haren ƴan bindiga za su fara barci ba tare da fargaba ba, domin jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu kan lamarin.
Gwamnan ya bayyana cewa ba ya damuwa idan ƴan adawa suna zagin sa a kafafen sada zumunta, amma ya sha alwashin ɗaukar mataki kan waɗanda suka mayar da aikinsu yaɗa ƙarya da siyasantar da batun tsaro a Jihar Kaduna.
"Nasarorin da muka samu ta hanyar matakan da ba na yaƙi ba suna bakanta ran mutanen da ba su damu da jin daɗin al’umma ba. Suna amfani da kafafen sada zumunta ne kawai don nuna fushinsu.”
“Siyasantar da rashin tsaro ba adawa ba ce, kuma jiga-jigan da ke yin hakan a kafafen sada zumunta ba sa damuwa da talakawa. Abin da suke yi kawai shi ne wallafa saƙonni domin cimma burinsu na siyasa."
- Gwamna Uba Sani
Gwamnati ta ɓullo da dabara kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ɓullo da wata sabuwar dabara domin magance matsalar rashin tsaro.
Gwamnatin ta ɓullo da sabuwar manhaja wacce mutane za su riƙa ba da rahoton ayyukan ta'addanci a yankunansu.
Asali: Legit.ng

