Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Sace Shugabannin APC a kan Hanyarsu Ta Zuwa Gidan Sanata
- 'Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da shugabannin APC biyar daga Kaura Namoda ta Kudu yayin da suke tafiya Mafara
- An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar 1 ga Maris, 2025 a yankin da ke Zamfara a Arewacin Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro
- Cikin wadanda aka sace akwai Yahaya Sani Dogon Kade, Shugaban Dan Isah Ward, da Bello Dealer, Shugaban Sakajiki Ward, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar
- 'Yan bindiga sun kai wa motocin APC hari a hanyarsu zuwa gidan Sanata Abdulaziz Yari, inda suka yi garkuwa da mutane biyar daga cikin tawagar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - 'Yan bindiga sun sace shugabannin APC biyar daga Kaura Namoda ta Kudu a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.
An ce maharan sun sace jiga-jigan ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Mafara a jihar Zamfara.

Asali: Original
Sojoji sun yi cafke kasurgumin dan bindiga
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne a ranar Asabar 1 ga Maris, 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan hari na zuwa ne kwana ɗaya bayan rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar damke wani kasurgurmin dan ta'adda, Kachallah Hassan Nabamamu wanda ya addabi Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan cafke shi, yaransa da wasu manyan 'yan ta'adda sun farmaki kauyuka da dama don neman a sake shi.
Ta'addanci: Rundunar sojoji ta yi gargadi mai tsauri
Sai dai rundunar ta bayyana cewa ba za ta lamunci wani dan ta'adda ya yi kokarin haramta wa jama'a zaman lafiya a sassan jihar ba.
Masana sun ce wannan nasara na da nasaba da irin matsin lamba da sojoji ke yiwa yan bindiga a kokarin ganin sun kakkabe su musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Sojojin na ci gaba da samun galaba kan yan bindiga a ƙoƙarinsu na murkushe tasirin rikakken ɗan ta'adda, Bello Turji.

Asali: Facebook
Zamfara: Yadda yan bindiga suka sace shugabannin APC
Wasu majiyoyin sirri sun shaida cewa cikin wadanda aka sace akwai Shugaban Dan Isah Ward, Yahaya Sani Dogon Kade, da Shugaban Sakajiki Ward, Bello Dealer.
An tabbatar cewa shugabannin APC da aka sace suna kan hanyarsu ta zuwa gidan Sanata Abdulaziz Abubakar Yari.
Daga nan ne 'yan bindiga suka tare su, suka kama mutum biyar daga cikin tawagar suka tsere da su.
Kasurgumin dan ta'adda ya mika wuya ga hukumomi
A jihar Katsina kuwa, mun ba ku labarin cewa yayin da sojoji ke kara kaimi wurin kakkabe yan ta'adda musamman Arewacin Najeriya, wasu rikakku sun mika wuya.
Daga cikinsu akwai fitaccen ɗan bindiga, Abu Radde, da yaransa inda miƙa wuya ga jami’an tsaro, suka saki mutum 10 da suka sace a yarjejeniyar zaman lafiya.
Majiyoyi sun ce Abu Radde da wasu ‘yan fashi sun nemi sulhu ta hanyar lumana tare da ganawa da jami’ai a Kwari a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina.
Asali: Legit.ng