"Kai Matsaroci ne": Minista Ya Yi Kaca Kaca da Mataimakin Abba kan Sukar Tinubu
- Ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane bai ji daɗin kalaman da mataimakin gwamnan Kano ya yi ba kan Bola Ahmed Tinubu
- Ministan ya bayyana kalaman Aminu Abdulsalam Gwarzo a matsayin rashin kunya da rashin girmama ofishin shugaban ƙasa
- Abdullahi Ata ya buƙaci mataimakin gwamnan da gwamnatin jihar Kano da su gaggauta janye furucin cikin awanni 72 masu zuwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya caccaki mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Yusuf Abdullahi Ata ya yi Allah wadai da kalaman da mataimakin gwamnan ya yi game da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, dangane da rikicin sarautar Kano.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin ministan, Seyi Olorunsola, ya fitar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a manta ba dai Aminu Abdulsalam Gwarzo ya nemi shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire sarkin da ya naɗa wanda ya ajiye a cikin maƙabarta.
Ministan Tinubu ya caccaki Aminu Gwarzo
Bisa hakan ne ministan ya buƙaci mataimakin gwamnan da kuma gwamnatin jihar Kano baki ɗaya, su janye furucinsu na wulakanci cikin awanni 72 masu zuwa.
Sannan su kuma bayar da haƙuri a hukumance ga shugaba Tinubu saboda furucin da mataimakin gwamnan ya yi.
Ministan ya ce idan ba su yi hakan ba, masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC za su ɗauki mataki ta hanyoyi na shari'a da siyasa waɗanda suka dace.
Haka kuma, ministan ya kira mataimakin gwamnan a matsayin matsoraci kan sukar Tinubu, inda ya bayyana kalamansa a matsayin rashin girmamawa.
Me aka ce kan mataimakin gwamnan Kano?
"Mataimakin gwamnan ya nuna rashin kunya wajen yin magana kan shugaban ƙasan Najeriya ta wannan hanya mara ladabi da rashin girmamawa."

Kara karanta wannan
Mataimakin shugaban Majalisa ya goyi bayan kudirin ƙirkiro jiha 1 a Arewa, an faɗi sunanta
"Hakan ba abin da za a yarda da shi ba ne, rashin kunya ne kuma cin mutuncin darajar ofishi mafi girma ne na ƙasa."
"Gwamnatin jihar Kano, ta hannun mataimakin gwamnan, ta sake nuna son zuciyarta wajen ƙin bin doka da kuma rashin girmama cibiyoyin dimokiradiyya."
"Wannan magana mai rashin hankali da rashin kula ta bayyana gazawar gwamnatin jihar Kano wajen fahimtar muhimmancin ƙa'idojin mulki da tsarin tarayya."
"Yana da muhimmanci mu tunatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf da gwamnatinsa cewa, ofishin shugaban ƙasa ba wani ɓangare ba ne na wasan siyasarsu ta cikin gida ba."
- Yusuf Abdullahi Ata
Shugaban APC ya caccaki ministan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya yi martani mai zafi ga ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane.
Abdullahi Abbas ya caccaki Yusuf Abdullahi ne bayan ya yi barazanar ficewa daga APC idan ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar.
Shugaban na APC ya bayyana cewa ba su san da zaman ministan ba domin ba ɗan jam'iyyar ba ne.
Ya nuna matuƙar mamakinsa kan yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi muƙamin minista a gwamnatinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

