Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Goyi Bayan Kudirin Kirkiro Jiha 1 a Arewa, An Faɗi Sunanta
- Snaata Barau Jibrin ya ayyana goyon bayansa ga kudirin kirkiro jihar Karaɗuwa wacce za a cire daga jihar Katsina a Arewa maso Yamma
- Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce zai haɗa kai da Sanata Muntari Ɗandutse wajen tabbatar da an cimma burin kirkiro jihar
- Sanata Muntari Ɗandutse ya rabawa mutanen mazaɓarsa tallafin kayan abinci saboda zuwan Ramadan, da kayan sana'o'i domin dogaro da kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana goyon bayansa ga kudirin samar da sabuwar jiha mai suna "Karaduwa" a jihar Katsina.
Sanata Barau ya faɗi hakan ne a ranar Asabar a wurin taron rabon tallafi a garin Funtua da ke Kudancin jihar Katsina a Arewa maso Yamma.

Asali: Facebook
Barau Jibrin ya ce zai yi aiki tare da Sanata Muntari Dan-Dutse, mai wakiltar Funtua a majalisar dattawa, domin ganin an cimma wannan buri, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan
"Karya kake yi," Ƴan Majalisa 36 sun ƙara yi wa kakaki bore, sun tabbatar da tsige shi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau ya goyi bayan kirkiro jihar Karaɗuwa
A cewarsa, ƙirƙirar sabuwar jiha zai kawo ci gaba mai ma'ana ga al’ummar yankin, tare da jawo ƙarin damammakin tattalin arziki da ci gaban rayuwa.
“Zan hada hannu da dan uwana, Sanata Muntari Dan-Dutse, domin tabbatar da samar da sabuwar jihar Karaduwa.
"Ina maraba da wannan bukata daga ƴan Karaɗuwa, domin suna da cikakken arzikin noma da dukkan abubuwan da ake bukata don zama jiha. Ko da yake yana da wahala, amma yana iya yiwuwa,” in ji shi.
Sanata Barau ya bayyana haka ne a wajen taron rabon kayan abinci na Ramadan da tallafa wa mata da matasa, wanda Sanata Muntari Dan-Dutse ya shirya.
Gwamma Dikko ya roki addu'a daga jama'a
A yayin taron, gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, wanda mataimakinsa, Hon. Faruk Jobe, ya wakilta, ya bukaci al’ummar da suka amfana da kayan abincin da kada su sayar da su.
Dikko Radda ya jaddada bukatar yin addu’a domin ci gaban jihar da kasa baki daya, musamman a wannan wata mai alfarma.
Gwamna Radda ya jero wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a bangarorin ilimi, kiwon lafiya, noma, tsaro da tattalin arziki.
A nasa jawabin, Sanata Muntari Dan-Dutse ya jaddada kudirinsa na kawo ci gaba duk da matsin tattalin arziki da matsalar tsaron da ake fuskanta.
Abubuwan alherin da Sanata Ɗandutse ke yi
A cewarsa, yana taka rawar gani wajen kawo wa al'ummarsa ci gaba da kayayyakin more rayuwa, musamman wajen kafa Jami’ar Kimiyya da Lafiya ta Tarayya a garin Funtua.
"Mun yi bakin ƙoƙarinmu wajen ganin an kafa jami’ar. Gwamnan Katsina ya ware Naira biliyan 3.5 domin fara aikin, ba a sa aikin a kasafin kudin 2024 amma mun yi kokari an saka shi a kasafin 2025.
"A kasafin kudin 2025 an sake ware masa kudade. An nada shugaban jami’ar da majalisar gudanarwa, sannan ana shirye-shiryen daukar ma’aikata,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Jerin Majalisun dokoki na jihohi 6 da aka sha fama da rikicin shugabanci a Najeriya
Ɗandutse ya ce, a kasafin kudin 2025, an ware Naira biliyan 5.7 don manyan ayyuka a jami’ar, tare da Naira biliyan 5 daga asusun TETFund, da kuma Naira biliyan 2.9 a matsayin tallafi na yau da kullum.
Sanata Ɗandutse ya raba kayan sana'o'i
A yayin taron, an raba kayan tallafi ga al’ummar mazabar Katsina ta Kudu, wanda ya shafi kananan hukumomi 11, Bakori, Musawa, Kankara, Kafur, Faskari, Matazu, Danja, Funtua, Dandume, Malumfashi da Sabuwa.
Kayan da aka rabawa mutane sun haɗa da buhunan shinkafa 3,795, buhunan masara 1,100, Keke Nafef 100, babura 350, keken ɗinki 384, injinan nuƙa 110 da sauransu.
Sanata Goje ya tallafawa mutanen Gombe
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Danjuma Goje (Gombe ta Tsakiya) ya sake tallafa wa al’ummar mazabarsa ta hanyar raba kekunan dinki da kudi domin bunkasa sana’o’in hannu.
Sanatan ya kuma bai wa kowane mutum da ya karbi keken dinki kudi har N20,000 domin taimaka musu wajen fara amfani da kayan aikin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng