Bayan Dangote, NNPCL Ya Yi Maganar Saukar Farashi Fetur da Kara Gidajen Mai

Bayan Dangote, NNPCL Ya Yi Maganar Saukar Farashi Fetur da Kara Gidajen Mai

  • Kamfanin NNPCL ya bayyana shirin kara adadin tashoshin mai daga 1,000 zuwa 2,000 kafin karshen shekarar 2025
  • NNPCL ya ce matatun mai na kasar suna aiki, banda sabon matatar Fatakwal da ta Kaduna da ake sa ran za su fara aiki nan gaba
  • Rahotanni sun nuna cewa NNPCL ya ce farashin man fetur zai ragu idan darajar Naira ta karu a kasuwar hada-hadar kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL a bayyana cewa yana da shirin kar adadin tashoshin mai da yake da su daga 1,000 zuwa 2,000 nan da karshen shekarar 2025.

Babban jami’in hulda da jama’a na kamfanin, Olufemi Soneye, ne ya bayyana hakan yayin wani taron hadin gwiwa da kwamitoci a majalisar tarayya da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai a Najeriya yayin da musulmi suka fara azumin watan Ramadan

NNPCL
Za a fadada gidajen man gwamnati a Najeriya. Hoto: NNPC Limited
Asali: Getty Images

Rahoton the Nation ya nuna cewa NNPCL na kokarin fadada kasuwancinsa a bangaren rarraba mai domin samar da saukin wahalar man fetur ga 'yan kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin kara yawan gidajen man NNPCL

A cewar Olufemi Soneye, kafin watan Oktoba na bara, NNPCL yana da tashoshin mai 897 a fadin Najeriya, amma a halin yanzu an kara yawan su zuwa fiye da 1,000.

Olufemi Soneye ya ce:

"NNPCL ne kamfani mafi girma a Afirka, kuma muna kokarin fadada kasuwancin man fetur a Najeriya.
Manufarmu ita ce kara yawan tashoshin zuwa 2,000 kafin shekarar 2025 ta kare."

Soneye ya bayyana cewa karin tashoshin zai taimaka wajen inganta wadatar man fetur a yankunan da ake fama da karancin sa.

NNPCL: Matafun man Najeriya na aiki

Soneye ya bayyana cewa matatun mai na NNPCL suna aiki tun farkon shekarar da ta gabata, ban da matatun Fatakwal da Kaduna da ake kan gyara su.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fitar da sanarwa kan ganin watan Ramadan na 2025

A cewar Soneye:

"Akwai matatun mai biyu a Fatakwal; tsohuwar tana aiki, amma sabuwar tana kan gyara.
"Haka nan ana kan gyara matatar Kaduna kuma muna sa ran za ta fara aiki kafin karshen 2025,"

Ya tabbatar da cewa kamfanin NNPCL yana kokarin ganin an samu wadatar mai ta hanyar amfani da matatun gida.

Magana kan raguwar farashin man fetur

Dangane da tsadar man fetur, Soneye ya bayyana cewa farashin mai a gida Najeriya yana da alaka da kasuwar duniya, kuma yana iya raguwa idan darajar Naira ta karu.

NNPCL
Shugaban NNPCL, Meye Kyari. Hoto: NNPC Limited
Asali: UGC

Soneye ya ce:

"A matsayinsa na kamfanin mai, NNPCL na iya shigo da mai don rage tsadar da ake fuskanta a kasuwa."

Ya kara da cewa dokar PIA ta bai wa kamfanonin kasuwancin mai ikon shigo da mai, don haka babu wani kamfani daya tilo da zai mamaye kasuwa.

Kamfanin MRS ya rage farashin man fetur

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan Najeriya za su yi tirjiya ga Tinubu kan karin kudin wuta

A wani rahoton, kun ji cewa kamfin mai na MRS ya sanar da rage farashin man fetur a dukkan gidajen man da ke karkashin kulawarsa a jihohin Najeriya.

Lamarin na zuwa ne bayan matatar Dangote ta rage farashin mai a Najeriya a makon da ya wuce saboda azumin watan Ramadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel