Sarakuna Sun Taru Sun ba Shugaba Bola Tinubu Mukamin Sarauta Mafi Girma

Sarakuna Sun Taru Sun ba Shugaba Bola Tinubu Mukamin Sarauta Mafi Girma

  • Rahotanni na nuna cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi sarautar gargajiya mafi girma a Akwa Ibom
  • Sarakunan gargajiya na jihar sun mika sarautar a fadar shugaban kasa tare da tawagar da Gwamna Umo Eno ya jagoranta
  • Tinubu ya bukaci hadin kan ‘yan siyasa don ciyar da kasa gaba, yana mai yabawa ci gaban da ake samu a Akwa Ibom

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi sarautar gargajiya mafi girma a Akwa Ibom da ake kira "Otuekong."

Rahotanni sun nuna cewa sarakunan gargajiya na jihar ne suka mika sarautar a wani bikin da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja, ranar Juma’a.

Tinubu
Tinubu ya zamo basarake a jihar Akwa Ibom. Hoto: Dada Olusegun
Asali: Facebook

Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya wallafa yadda aka ba Bola Tinubu sarautar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar da ta jagoranci wannan biki ta kunshi Gwamna Umo Eno, sarakuna, manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da kuma kungiyoyin addini, matasa da mata.

Bola Tinubu ya bukaci hadin kan ‘yan siyasa

Bayan karbar sarautar, Tinubu ya bayyana jin dadinsa da wannan karamci, yana mai tunawa da zamansa a Eket a lokacin da yake aiki da kamfanin Mobil.

Shugaban kasar ya ce:

"Ni ɗaya ne daga cikinku. Mun zama 'yan uwa da abokai, kuma na shaida yadda Akwa Ibom ke ci gaba da bunkasa da sauri."

Shugaban kasar ya ce Najeriya za ta fi samun ci gaba idan shugabanni sun daina fifita bambancin jam’iyya, kuma suka mai da hankali kan ci gaban kasa gaba daya.

Tinubu ya yabi gwamnan Akwa Ibom, Eno

Tinubu ya jinjina wa Gwamna Umo Eno bisa yadda yake tafiyar da jagorancinsa cikin adalci da hangen nesa.

Bola Tinubu ya ce:

Kara karanta wannan

Natasha: Atiku ya tsoma baki a zargin shugaban majalisa da neman lalata

"Gwamnanku yana kyakkyawan shugabanci kuma yana da tsoron Allah. Na kan bi shirye-shiryen da ake gabatarwa daga jiharku, kuma ina kallon irin cigaban da ake samu."

Shugaban kasar ya kuma tabbatar da cewa ya saurari koke-koken gwamnan kan gina tashar jiragen ruwa da kuma bukatar ziyarar aiki zuwa jihar.

Gwamna Eno ya jaddada goyon baya ga Tinubu

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya kasance a taron, ya yabawa Gwamna Eno bisa kokarin hada kan ‘yan siyasa a jihar.

Ya ce:

"Za mu ci gaba da hadin kai domin ciyar da jihar gaba, kuma muna goyon bayan gwamnatin Shugaba Tinubu don bunkasa Najeriya."

Shi ma Gwamna Eno ya bayyana kudirinsa na yin aiki tare da gwamnatin tarayya, musamman wajen bunkasa manyan ayyuka kamar tashar jiragen ruwa da kuma warware matsalolin muhalli.

Tasirin matakin ga siyasar yankin

Masana harkokin siyasa na ganin cewa karbar wannan sarauta da Tinubu ya yi na iya kara inganta dangantaka da jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan saukar farashin abinci, ya yi alkawarin karin sauki

Kazalika, hadin kan ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban a wannan taro na iya zama matakin kawo hadin kai a yankin Kudu maso Kudu.

An yi barazanar zanga zanga ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan kasuwa da kungiyoyi sun gargadi Bola Tinubu kan maganar karin kudin wuta da ake zargin ana shirin yi a kasar nan.

Kungiyoyi sun ce lamarin zai iya durkusa sana'o'i da kuma rage ciniki a kasuwanni, sun kuma yi barazanar fara zanga zanga idan Tinubu bai dakatar da karin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng