Matsala ta Kunno Kai a Najeriya yayin da Musulmi Suka Fara Azumin Watan Ramadan
- Da yiwuwar a shiga matsalar ƙarancin mai da rasa ayyukan yi da matakin hana amfani da tankoki masu cin lita 60,000 ya fara aiki
- Kwanan nan hukumar NMDPRA ta haramta amfani da manyan tankokin a titunan Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris, 2025
- Wannan matsala dai ta kunno kai ne a daidai lokacin da musulmin Najeriya suka fara azumin watan Ramadan na shekarar bana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ana fargabar shiga matsalar karancin man fetur yayin da haramcin amfani da tankoki masu cin lita 60,000 ya fara aiki a yau, 1 ga Maris, 2025.
Hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa watau NMDPRA ce ta sanar da haramta amfani da tankokin a titunan Najeriya a makon da ya gabata.

Asali: Getty Images
Kamar yadda Daily Trust ta kawo, hukumar ta ce hakan zai taimaka wajen rage hadurran gobara da asarar rayuka da ke faruwa sakamakon hatsarin motocin dakon mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin na iya haifar da ƙarancin mai
Bayan haramcin da ya fara aiki yau, za a dakatar da motocin da ke daukar fiye da lita 45,000 daga lodin man fetur a karshen shekarar 2025.
Sai dai, kungiyar masu tankoki (NARTO), ta nuna damuwa kan matakin, tana mai cewa masu jarin da suka zuba fiye da Naira biliyan 300 a irin motocin na iya fuskantar gagarumar asara.
Sakataren NARTO, Aloga Ogbogo, ya ce suna jiran su ga yadda aiwatar da dokar za ta kasance kafin su fadi matsayarsu.
Wani 'dan NARTO, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:
"Wannan ba abu ne mai kyau ga masu jarin da suka kashe kudinsu wajen shigo da wadannan tankoki ba. Meyasa NMDPRA suka amince da shigowarsu tun farko, idan da gaske suna son haramta su?"
Masu harkar mai za su rasa aikin yi
Wasu direbobi sun nuna damuwarsu kan yadda dokar za ta shafi farashin man fetur da kuma aikin direbobin tankuna.

Kara karanta wannan
Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur
Alhassan Gambo, direban tankar mai da ke tuka mota daga Kano zuwa Lagos, Fatakwal da Warri, sama da shekaru 11 da suka wuce, ya ce:
"Ba na tunanin za a samu matsalar karancin mai sosai, amma tabbas za a samu karin farashi saboda adadin man da ake dauka zai ragu, amma kudin sufuri zai kasance iri daya."

Asali: UGC
Shi ma wani direba, Usman Small, ya bayyana cewa:
"Za a samu karancin man fetur da sauran kayayyakin mai saboda wadannan motocin na da muhimmanci sosai wajen wadatar da kasuwa da isar da kaya a cikin sauki."
Masana harkokin sufuri da makamashi sun yi gargadi cewa idan gwamnati ba ta dauki matakan sassautawa ba, dokar na iya haifar da karancin man fetur, tashin farashi, da kuma barazanar rasa ayyukan yi ga direbobi.
Gwamnati ta rufe gidajen mai a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NMDPRA ta garkame gidajen mai biyar a jihar Katsina, ba wannan ne karon farko da aka fara yin wannan ba.
Wannan matakin ya biyo bayan binciken da hukumar ke gudanarwa don tabbatar da cewa gidajen mai suna bin ka’idojin aiki da kare hakkin masu sayen mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng