Kano da Jihohin Arewa Sun Fara Azumin Ramadan da Ƙafar Dama, Saudi Ta Turo Tallafi
- Yayin da aka fara azumin watan Ramadan a yau Asabar, Saudiyya ta miƙa tallafin tan 50 na dabino ga gwamnatin Kano da jihohin Arewacin Najeriya
- Ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano ya ce wannan tallafi wani ɓangare ne na ayyukan jin ƙai da ƙasa mai tsarki ta saba gudanarwa duk shekara
- Wakilan masarautar Saudiyya sun raba katan-katan na dabino a taron miƙa tallafin wanda ya gudana jiya Juma'a a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Ofishin jakadancin Masarautar Saudiyya ya raba katan-katan na dabino 1,250 ga gwamnatin Kano da wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Saudiyya ta ba da wannan tallafi na jimullar dabino tan 50 domin a rabawa musulmi a Kano da jihohin Arewa a wani ɓangare na taimakon da ta saba bayarwa a kowace shekara.

Asali: Twitter
Leadership ta tattaro cewa wakilan ƙasar Saudiyya sun raba dabinon ne a wani taro da aka shirya a jihar Kano jiya Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da musulmi suka fara azumin watan Ramadan bayan fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi ta tabbatar da ganin wata.
Bikin rarraba dabinon ya gudana a Kano jiya, inda kungiyoyin addini, marasa galihu, da gidajen marayu suka amfana da wannan tallafi.
Ramadan: Saudiyya ta bada tallafin dabino
Wannan tallafi na dabino ya fito ne daga cibiyar agaji da jin ƙai ta Sarki Salman na ƙasar Saudiyya (KSrelief), kuma an ba Kano da jihohin Arewa kyautar tan 50 na dabino.
Cibiyar ta ɗauki nauyin ba da tallafin ne domin taimakon iyalai mabuƙata da kuma kara karfafa dangantakar dake tsakanin Saudiyya da Najeriya.
Jakadan Masarautar Saudiyya a Kano, Khalil Adamawy, ya jaddada cewa ƙasarsa na da ƙudirin ci gaba da bayar da taimako ga al'umma musamman marasa ƙarfi.
"Ina mika godiyata ga Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mohammed bin Salman bisa jajircewarsu wajen taimakawa Musulmi da mabukata a duniya."
Ya kara da cewa Saudiyya za ta ci gaba da bayar da tallafi don karfafa hadin kai na addinin Musulunci da kuma rage radadin wahala ga al’ummomi.
"A bana, an raba tan-tan na dabino a Abuja makon da ya gabata, yayin da ake ci gaba da shirin rarraba wasu tan 50 na dabino a nan jihar Kano da wasu jihohin Arewacin Najeriya," in ji shi.

Asali: Facebook
Gwamnatin Kano ta godewa Saudiyya
Da yake karbar tallafin a madadin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, sakataren gwamnatin jihar (SSG), Faruk Ibrahim, ya nuna godiya ga hukumomin Saudiyya bisa wannan kyauta.
Ya bayyana cewa wannan taimako zai kara karfafa dangantakar da ke tsakanin Kano da Saudiyya, rahoton PR Nigeria.
Wannan tallafi na dabino na daga cikin kyaututtuka da tallafin jin kai da Saudiyya ke bayarwa domin taimakawa Musulmi da mabuƙata a fadin duniya.
An ga watan Ramadan a Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa an ga jinjirin watan Ramadan a ƙasar Saudiyya ranar Juma'a, 28 ga watan Fabrairu, 2025 daidai da 29 ga watan Sha'aban, 1446H.
A wata sanarwa da hukumomin Saudiyya suka fitar, an umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi su tashi da azumi ranar Asabar, 1 ga watan Maris 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng