Ramadan: Tinubu Ya Tura Sako ga Musulmi, Ya Yi Albashir kan Farashin Abinci da Fetur

Ramadan: Tinubu Ya Tura Sako ga Musulmi, Ya Yi Albashir kan Farashin Abinci da Fetur

  • Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da aniyar gwamnati wajen bunkasa noma da wadatar abinci yayin da Musulmai ke fara azumin Ramadan na 2025
  • Tinubu ya bayyana Ramadan a matsayin lokaci na ibada, tausayi, da hadin kai, yana kira ga 'yan kasa da su yi addu'a don zaman lafiya da ci gaba
  • Shugaban ya ce manufofinsa na kawo sauyi sun fara yin tasiri, inda tattalin arziki ke daidaituwa, farashin abinci na raguwa, haka zalika kudin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sakon taya murna ga al'ummar Najeriya yayin da ake shirin fara azumin watan Ramadan.

Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na inganta harkar noma da tabbatar da wadatar abinci ga 'yan Najeriya yayin azumin Ramadan na shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Bayan duba wata, Sarkin Musulmi ya fadi ranar fara azumin Ramadan a Najeriya

Tinubu ya tura sako na musamman ga Musulmi saboda azumin Ramadan
Bola Tinubu ya taya al'ummar Musulmi murnar fara azumin watan Ramadan. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Alkawuran da Tinubu ya daukarwa yan Najeriya

Wannan na kunshe a cikin sakon da ya aikawa al’ummar Musulmi a ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairun 2025, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnati na daukar matakai don bunkasa noma da karfafa wadatar abinci da fatattakar 'yunwa.

Tinubu ya ce:

"Yayin da damina ke karatowa, muna kokarin bunkasa harkar noma, za mu karfafa wadatar abinci ta hanyar tallafi, injiniyanci, da sababbin dabarun noma."

Tinubu ya bayyana Ramadan a matsayin lokaci na ibada, hakuri, da tausayi ga marasa karfi, ya bukaci Musulmi su dauki darasin ibada da sadaukarwa.

Shugaban ya ce manufofin gwamnatinsa na kawo ci gaba sun fara yin tasiri, yana mai cewa alamu na nuna cigaban tattalin arziki, Vanguard ta ruwaito.

Bola Tinubu ya yi albashir ga al'ummar Musulmi game da watan Ramadan
Tinubu ya ba yan tabbacin kawo sauki a kasa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya ba yan Najeriya shawara kan Ramadan

Ya ce:

"Ramadan lokaci ne na tunani, kara kusanci da Allah, da aikata ayyukan alheri, mu yi amfani da lokacin don hadin kai da zaman lafiya."

Kara karanta wannan

Ramadan: 'Dan majalisa ya jika limamai da N40m, ya raba buhunan abinci 1,000

"Wannan Ramadan na musamman ne domin yana zuwa daidai da lokacin da kasar mu ke samun ci gaba, manufofinmu sun fara inganta tattalin arziki."

Ya bayyana cewa GDP na karshen 2024 ya karu, farashin abinci yana raguwa, kuma canjin kudi yana samun daidaito.

Haka kuma, ya ce saukar farashin mai yana nuna alamun farfadowar tattalin arziki.

Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su yi amfani da watan azumi don yin addu'a ga ci gaban kasa da hadin kai.

Ya kara cewa:

"Ina kira ga kowa da kowa da mu hada kai wajen addu’a da aiki don ci gaban kasa, mu tabbatar kalmominmu da ayyukanmu na nuna hadin kai.
"Allah ya albarkaci wannan wata, ya sa ya zama na alheri gare mu duka, kuma ya kara mana karfi da hadin kai a matsayin kasa."

Ya aika da fatan alheri ga Musulmai da ke azumi, yana mai fatan watan ya kasance mai cike da albarka da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan saukar farashin abinci, ya yi alkawarin karin sauki

APC ta marawa Tinubu baya kan zaben 2027

Kun ji cewa jam'iyyar APC ta nuna gamsuwa game da salon mulkin shugaba Bola Tinubu a Najeriya tare da ba shi tabbaci kan zaben 2027.

APC ta hade wuri guda wajen bayyana gamsuwa da yadda Tinubu ke tafiyar da mulkinsa a kasar duba da nasarorin da ake samu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel