Natasha: Atiku Ya Tsoma Baki a Zargin Shugaban Majalisa da Neman Lalata

Natasha: Atiku Ya Tsoma Baki a Zargin Shugaban Majalisa da Neman Lalata

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana takaici a kan yadda aka samu zargin cin zarafi a majalisar dattawa
  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ce Shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya sha nemanta da lalata
  • Ta bayyana cewa rashin amince wa wajen ba shugaban hadin kai ne silar wasu daga cikin abubuwan da Akpabio ke mata a zauren majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan zarge-zargen cin zarafi, tsoratarwa, da rashin adalci da ake yi a kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta zargi Shugaban Majalisar Dattawan da yin kalaman da ba su dace ba, tare da cewa ya bukaci ta "ba shi kula wa."

Kara karanta wannan

'Ba haka ba ne': Matar Akpabio ta yi barazana ga Natasha, ta fallasa tsohuwar alakarsu

Majalisa
Atiku na son a gudanar da bincike a kan zargin 'yar majalisa Hoto: Godswill Obot Akpabio/@NGRSenate
Asali: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kuma a cikin gaskiya da adalci a kan abin da ya kira zarge-zarge masu tayar da hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio/Natasha: Atiku ya nemi daukin Tinubu

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci shugaba Bola Tinubu da ya saka baki a cikin dambarwar da ke gudana a tsakanin Akpabio da takwararsa Natasha.

Atiku ya ce:

"Tun da mata hudu ne kacal ke cikin Majalisar Dattawa a halin yanzu, dole ne mu samar da yanayi da zai ba su damar aiki ba tare da tsoro ko cin zarafi ba.
"Wannan lokaci na bukatar daukar mataki domim kare mutuncin hukumominmu da tabbatar da cewa kowane dan Najeriya, ba tare da la’akari da jinsinsa ba, yana samun mutuntawa da hakkinsa."

Atiku ya son a binciki zargin Sanata Natasha

A cewar jagoran a jam'iyyar adawa ta PDP, wadannan zarge-zarge na da matukar girma, kuma sun cancanci a gudanar da bincike mai zurfi, mai adalci, da kuma da gaskiya a nan kusa.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisa ya yi magana kan zargin ya nemi yin 'lalata' da Sanata Natasha

Ya ce:

"Majalisar Dattawa ta na wakiltar muradun al’umma. Wadanda ke cikinta, musamman shugabanninta, dole ne su kasance masu rikon amana, mutunci, da girmama ofishinsu da kuma ‘yan Najeriya da suke wakilta.
"A matsayinsa na mutum na uku mafi karfi a kasar nan, ya kamata Shugaban Majalisar Dattawa ya zama misali na hali nagari da gaskiya."

Atiku ya nuna rashin jin dadin zargin cin zarafi

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zargin cin zarafin mata a wuraren aiki babbar barazana ce gare su.

Atiku
Atiku ya ce cin zarafin mata babbar matsala ce Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ce:

"Cin zarafin mata ta fuskar neman lalata da su a wurin aiki babbar matsala ce da ke hana su samun ci gaba, kuma hakan yana dakile cigaban kasa baki daya. Ba za a yi watsi da irin wadannan zarge-zarge ba, musamman idan sun shafi jami’in gwamnati da ke da karfin iko, tasiri, da nauyin da ya rataya a wuyansa."

Kara karanta wannan

Natasha: Yadda tsohuwar shugabar NDDC ta mari Akpabio kan zargin lalata a 2020

"Yadda za a tafiyar da wannan lamari zai aika da sako mai karfi game da yadda Najeriya ke daukar batun adalci da kuma bai wa mata damar shiga cikin shugabanci."

Shugaban majalisa ya magantu kan zargin lalata

A baya, mun kawo labarin cewa shugaban majalisa, Sanata Godswill Akpabio ya ce babu kamshin gaskiya a cikin zargin da Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha ta yi masa.

Sanata Akpoti-Uduaghan ta yi ikirarin cewa Sanata Akpabio yana watsi da kudirorin da take gabatar wa, da ajiye ta a gefe a wasu manyan abubuwa saboda ta ki aminta ya kusance ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel