Ana Shirin Fara Azumin Ramadan, Mutane Sama da 15 Sun Mutu a Jihar Katsina

Ana Shirin Fara Azumin Ramadan, Mutane Sama da 15 Sun Mutu a Jihar Katsina

  • Miyagun ƴan bindiga sun shiga kauyuka a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina, sun kashe akalla mutane 17
  • Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa ƴan ta'addan sun yi awon gaba da wasu mutane da dama da dabbobi masu yawa
  • Kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda amma mutane sun roki gwamnati ta kawo masu ɗauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Akalla mutane 17 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wasu munanan hare-hare da ƴan bindiga suka kai a kauyukan jihar Katsina ana shirin fara azumi.

Ƴan bindigar sun kuma sace mutane da dama da har yanzu ba a tantance adadinsu ba a yankin ƙaramar hukumar Faskari.

Gwamna Dikko Radda.
Yan bindiga sun kashe mutane 17 ana shirin azumi a jihar Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Ph D
Asali: Facebook

Yan bindiga sun shiga kauyukan Katsina

Rahotan Leadership ya nuna cewa harin wanda ya faru a ranar Litinin, ya shafi kauyukan Radama, Ungwan Baki, Ungwan Buntu, Mai Daura, da Yar Mai Kakgo.

Kara karanta wannan

Neja: 'Yan bindiga sun farmaki Musulmai ana shirin fara azumi, an rasa rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun shiga garuruwan ne a kan babura kusan 50, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi, suka kashe mazauna yankin da dama.

Cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wasu ‘yan sa-kai da ke kokarin kare al’ummarsu.

An ce mutane biyar ne aka kashe a Ungwan Buntu, yayin da wasu da dama suka jikkata kuma aka garzaya da su asibiti don jinya.

Baya ga haka, ƴan bindigan sun yi awon gaba da dabbobi da kayayyaki sannan suka sace wasu mazauna kauyuka daban-daban.

Yadda ƴan bindiga suka sace dabbobi

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa daya daga cikin shugabannin ‘yan bindigar ya bi ta garin Dankama yayin da yake shirin shiga dajin Yar-Tsamiya da dabbobin da suka sata.

"Abin bakin ciki shi ne yadda aka ga gangamin dabbobi da aka sace a wannan hari. Mutanen Fankama sun ce ba su taɓa ganin dabbobi masu yawa da aka sace a lokaci guda kamar haka ba," in ji wata majiya.

Kara karanta wannan

Dakaru sun yi dirar mikiya a kan 'yan ta'adda ana tsaka da karbar kudin fansa

Mutane sun roki gwamnati ta ɗauki mataki

Mazauna yankin sun nuna takaicinsu kan abin da suka kira sakacin matakan gwamnati kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

"Wannan bala'i ne da ya addabi jama’a. Mutane na mutuwa amma ba mu ga wani mataki mai karfi daga mahukunta ba," in ji wani mazaunin yankin.

Al’ummar yankin sun sake yin kira ga Gwamna Dikko Umaru Radda da ya dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Tsaro shi ne ginshikin duk wata al’umma. Idan babu tsaro, mutane ba za su iya rayuwa cikin kwanciyar hankali ba,” in ji wani jagoran al’umma.

Duk kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Sadiq Abubakar, bai yi nasara ba, domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto, bai amsa sakon da aka tura masa ba.

Yan bindiga sun kashe mutane a Neja

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun kashe mutane a yankin ƙaramar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ritsa 'yan bindiga a maboyarsu, an kama 'yan ta'adda 20

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce an yi wa mutanen kisan gilla, wanda ko kare ba zai ci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262