Ramadan: Ɗan Majalisa a Arewa Ya Tara Talakawa, Ya Raba Masu Kayan Abinci da Kudi
- Hon. Usman Zannah, ɗan majalisar Kaga/Magumeri/Gubio, ya ba da tallafi ga al’ummarsa domin rage wahalhalu musamman a Ramadan
- Kayan tallafin sun haɗa da shinkafa, sukari, taliya da kudi, wanda ya ce ya saba rabawa domin al'umma su yi azumi cikin walwala
- Hon. Zannah ya yi alkawarin ci gaba da bunkasa ilimi, aikin gona, da sanar da ayyukan yi domin inganta rayuwar talakawa a mazabarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Ɗan majalisar Kaga/Magumeri/Gubio (Borno) a majalisar wakilai, Hon. Usman Zannah, ya raba tallafin abinci ga mutane 5,000 a mazabarsa.
Kayayyakin tallafin sun hada da buhunan shinkafa, sukari, katan-katan na taliya da kayan girki, tare da gudummawar kudi don rage radadin tattalin arziki.

Asali: Twitter
'Dan majalisa ya rabawa talakawa 5000 tallafi
Hon. Usman Zannah, shugaban kwamitin majalisa na hukumar NEDC, ya ce ya raba tallafin ne domin ragewa jama'arsa wahalhalu, musamman a watan Ramadan, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da gwamnan Borno, Babagana Zulum, bisa kokarinsu na wanzar da zaman lafiya a yankin.
Hon. Zannah ya jaddada cewa an zabi wadanda suka ci gajiyar tallafin ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko kabila ba, domin hada kan al’umma.
Dalilin tallafawa mutane a lokacin Ramadan
Dan majalisar ya ce:
“Watan Ramadan wata ne da aka saukar da Al-Qur’ani, wanda ke matsayin shiriya da rahama ga masu kyautatawa."
Ya kara da cewa ya saba bayar da tallafi a irin wannan lokaci domin ragewa al'ummarsa wahalhalu, musamman ga talakawa a mazabarsa.
“Mutanena sun ba ni dama na wakilce su a majalisa, kuma ko da na bayar da dukiyata gaba daya, ba zai wadatar da amanar da suka dora mani ba.”
- Hon. Zannah.
Hon. Zannah ya bayyana cewa ba tun yanzu ne ya fara ba da tallafin ba, domin ya dade yana taimakon al’umma da kayan abinci, kayan sawa da kudi don rage radadin rayuwa.

Asali: Twitter
Ciyamomi sun jinjinawa dan majalisa
Ya bukaci mutanen mazabarsa da su kara hakuri da kuma yi masa addu’a domin ya ci gaba da wakiltarsu yadda ya kamata.
Zannah ya yi alkawarin kokarin bunkasa harkar ilimi, aikin gona, rage talauci, samar da ayyukan yi da inganta hanyoyi, ruwan sha, wutar lantarki da tsaro.
Ya yabawa Gwamna Babagana Zulum bisa mayar da Kwalejin Fasaha ta Kiwon Lafiya zuwa Magumeri, gina sababbin gidaje 50 da gyaran asibitocin Magumeri da Gubio.
Shugaban karamar hukumar Magumeri, Hon. Abubakar Abdulkadir (Bukar Yaro), ya yabawa dan majalisar bisa kokarinsa a mazabar.
Shugabannin kananan hukumomin Gubio da Kaga, Hon. Mali Bulama Mali Gubio da Hon. Mairu Abdallah (wanda mataimakinsa ya wakilta), sun gode masa bisa wannan tallafi.
'Dan majalisar Sokoto ya raba miliyoyin Naira
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'dan majalisar wakilai, Abdussamad Dasuki, ya bayar da tallafin N100m domin taimakawa mutanen mazabarsa a jihar Sokoto.
An kafa kwamitin mutum 35, wanda ya haɗa da limamai da shugabanni, domin rarraba kayan agaji ga al’ummar mazabar kafin fara azumin watan Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng