Natasha: Yadda Tsohuwar Shugabar NDDC Ta Mari Akpabio kan Zargin Lalata a 2020

Natasha: Yadda Tsohuwar Shugabar NDDC Ta Mari Akpabio kan Zargin Lalata a 2020

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na fuskantar zargin neman lalata daga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
  • A baya, tsohuwar shugabar NDDC, Joy Nunieh, ta zargi Akpabio da cin zarafi inda ta ce ta mare shi a gidansa a Apo a Abuja
  • Akpabio ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, ya ce an cire Nunieh daga mukaminta ne saboda dalilin rashin da’a
  • Wannan na zuwa ne bayan arangama da ta faru tsakanin Natasha da shugaban majalisa, Godswill Akpabio a makon jiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tsinci kansa cikin wata sabuwar takaddama kan zargin cin zarafi.

A baya, tsohuwar shugabar hukumar NDDC, Joy Nunieh, ta taba zargin Akpabio da cin zarafi, ta ce har zabga masa mari ta yi a gidansa da ke Apo bayan ya matsa mata.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisa ya yi magana kan zargin ya nemi yin 'lalata' da Sanata Natasha

Bayan Natasha, wata ta zargi Akpabio da neman lalata da ita
Yadda aka zargi Akpabio da neman alaka da tsohuwar shugabar hukumar NDDC. Hoto: Senator Natasha Akpoti-Uduaghan, Godswill Obot Akpabio.
Asali: Twitter

Wane zargi Sanata Natasha ta yi wa Akpabio?

Daily Trust ta tuna cewa shekaru biyar da suka gabata, yayin da Akpabio ke Ministan Harkokin Yankin Neja-Delta, Joy Nunieh, ta zarge shi da cin zarafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan zargin Sanata Natasha kan Akpabio da ta ce rigimar ta fara ne tun bayan da ya nemi lalata da ita.

Natasha ta bayyana a wani shirin talabijin cewa tana zargin Akpabio da neman lalata da ita kafin ta samu damar magana a zauren majalisa.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto Akpabio bai mayar da martani kan wannan zargi da Sanata Natasha ta yi ba tukuna.

Mai magana da yawunsa, Jackson Udom, bai amsa kiran da yan jaridu suka ta yi masa a safiyar ranar Juma’a ba.

Yadda tsohuwar shugabar NDDC ta mari Akpabio kan zargin neman lalata da ita

Yadda wata mata ta zabgawa Akpabio mari

A wancan lokaci, ita ma Nunieh ta yi irin wannan zargi a wannan gidan talabijin da Natasha ta yi nata.

Kara karanta wannan

Sanata ta yi tone tone kan alakar Natasha da Akpabio, ta fadi fifikon da yake ba ta a majalisa

A cikin kalamanta, ta yi zargin cewa Akpabio ya nemi ta karbi kudi ko kuma ya yi mata fyade, cewar TheCable.

Ta ce:

“Meyasa bai fada wa ’yan Najeriya cewa na mare shi a gidansa a Apo ba? Ni ce kadai mace da ta taba marin sa.
“Ban damu da kudi ba, ya ce zai tabbatar mani da mukamin shugabar NDDC, amma ni ba yarinya ba ce, na mare shi."

Sai dai Akpabio ya mayar da martani, yana cewa Nunieh tana da matsala a dabi'unta, har ya ce kamata ya yi ta tafi asibiti don duba lafiyarta.

Ya kuma musanta cewa an cire ta daga mukaminta saboda cin hanci, ya ce an sauke ta ne saboda rashin biyayya da rashin da’a wajen aiki.

Akpabio ya fusata bayan rigima da Natasha

A baya, kun ji cewa rikici ya barke a majalisar dattawa yayin da aka matsar da kujerar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, amma ta ki amincewa da hakan.

Kara karanta wannan

'Akpabio ya neme ni da lalata': Sanata Natasha ta tona asirin shugaban majalisa

Shugaban majalisa, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci fitar da Natasha daga Majalisa bayan ta ki bin umarnin da aka ba ta.

Rikicin ya tsananta lokacin da jami’an tsaro suka kewaye Natasha domin fitar da ita daga zauren majalisa bayan gardama mai zafi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.