'Akpabio Ya Neme Ni da Lalata': Sanata Natasha Ta Tona Asirin Shugaban Majalisa
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da yunkurin yin lalata da ita, ta ce tana da hujjoji
- Zargin ya biyo bayan takaddamar da ta barke tsakanin Natasha da Akpabio kan canza kujerar 'yan majalisa, wanda ta ce ba ta yarda ba
- Sanatar ta Kogi ta Tsakiya ta ce tana da hujjoji, ciki har da sakonnin WhatsApp, inda Akpabio ya bukaci su rika shakatawa tare a gidansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da yunkurin yin lalata da ita.
Natasha dai Sanata ce mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, kuma ta shiga majalisar ne bayan zaben shekarar 2023.

Asali: Facebook
Rigima ta kaure tsakanin Natasha da Akpabio
A wata hira da ta yi da Arise TV a ranar Juma’a, sanatar ta bayyana cewa tana da kwararan hujjoji kan zargin da take yi, tare da tabbatar da cewa mijinta ma shaida ne.

Kara karanta wannan
Sanata ta yi tone tone kan alakar Natasha da Akpabio, ta fadi fifikon da yake ba ta a majalisa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko, Sanata Natasha ta samu sabani da Akpabio bayan da ta gano an canza kujerarta ba tare da izini ba.
Wannan ya haddasa cacar baki a cikin zauren majalisa, wanda daga bisani ya kai ga tura ta kwamitin ladabtarwa don bincike.
Kwamitin, wanda Sanata Neda Imaseun (LP, Edo ta Kudu) ke jagoranta, an ba shi makonni biyu don gabatar da rahotonsa kan binciken halayen Natasha.
Bayan matakin majalisar ne, Sanata Natasha ta shigar da kara kotu, tana neman Akpabio ya biya ta diyyar Naira biliyan 100.3 kan take hakkinta.
Natasha ta tona asirin Akpabio a idon duniya
A cikin hirarta, Sanata Natasha ta ce tana da hotunan tattaunawarta da Akpabio, tana mai kalubalantar hukumar DSS da ta binciki sakonnin, ta ce "ya kan kira ni ta WhatsApp."

Asali: Facebook
Ta bayyana cewa batun ya samo asali ne tun 8 ga Disambar 2023, lokacin da ita da mijinta suka ziyarci Akwa Ibom don bikin zagayowar ranar haihuwar Akpabio.
"Komai ya fara ne ana gobe za a yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa da nawa, saboda a rana daya aka haife mu. Dukkanmu mun je Akwa Ibom.
"Da farko, mun fara zuwa gidansa da ke Ikot Ekpene. Sannan mu ka je wani gidansa da ke Uyo, ya rike hannuna, muka rika zagaya gidan, daki bayan daki, ya nuna mun yadda gidan ya kayatu.
"Ya kai ni wani kayataccen falon baki, inda ya tambaye ni ko gidansa ya burge ni. Na ce masa kwarai kuwa, ranka ya dade, dakunan sun yi kyau sosai.
"Sai ya ce da ni, yanzu kin zama sanata, zan rika ware lokacin da za mu rika zuwa nan muna hutawa. Za ki ji dadin hakan. A wannan gabar ne, na janye daga gare shi, saboda ban fahimci me yake nufi ba.
"Da muka koma gida, mijina ya gargade ni a kan kada in rika tafiya wata kasar waje ni kadai ko in kasance tare da shugaban majalisar dattawan shi kadai."
- Sanata Natasha.
Ta kwatanta lamarin da yadda dalibai mata ke fuskantar hukunci mai tsanani daga malamin da ya nemi yin lalata da su amma suka ki amincewa.
Har yanzu, Akpabio bai mayar da martani kan wannan zargi ba, duk da cewa batun na cigaba da yaduwa a kafafen sada zumunta.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Sanata Natasha ta shirya yin fallasa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta amince za ta tattauna da manema labarai kan takaddamarta da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa ta bayyana cewa ta shirya yin magana kan gaskiyar abin da ya jawo fadanta da Akpabio.
Natasha Akpoti ta nuna shirinta na fuskantar kwamitin bincike da aka kafa kan taƙaddamarta da Godswill Akpabio a zauren majalisa bayan ta maka shi kotu kan zargin cin fuska.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng