Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, Sun Kashe 217, An Kama Miyagu 574

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, Sun Kashe 217, An Kama Miyagu 574

  • Rahotanni na nuni da cewa rundunar sojin Najeriya ta kashe ‘yan ta’adda 217 tare da cafke wasu 574 a watan Fabrairu 2025
  • Haka zalika, sojojin sun ceto mutane 320 da ke hannun ‘yan ta’adda, yayin da 152 daga cikinsu suka mika wuya ga hukuma
  • Baya ga haka, an kama mutane 122 masu satar danyen mai, an kuma kwato kayayyakin sata na sama da Naira biliyan 2.1

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a yaki da ta’addanci da fashi da makami a watan Fabrairun 2025.

Hedikwatar Tsaro ta kasa (DHQ) ce ta sanar da hakan ta bakin Daraktan Yada Labarai na Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Sojoji
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 217 a watan Fabrairu. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa, a cikin watan Fabrairu kadai, sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 217, sun kama wasu 574, sannan wasu 152 sun mika wuya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ceto mutane 320 wajen ‘yan ta’adda

Bayan kashewa da kama ‘yan ta’adda, sojoji sun kuma kubutar da mutane 320 da ke tsare a hannun ‘yan ta’adda a yankuna daban-daban.

Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara a ayyukan da sojoji ke yi na kai farmaki a fadin kasar nan, musamman a Arewa da yankin Neja-Delta.

Ya ce sojojin sun ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda, wanda hakan ya sa wasu daga cikinsu suka mika wuya ba tare da an yi musu barazana ba.

An kwato makamai masu yawa

A yayin da sojoji ke ci gaba da aikin tabbatar da tsaro, sun kwato makamai da harsasai masu yawa daga hannun ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Dakaru sun yi dirar mikiya a kan 'yan ta'adda ana tsaka da karbar kudin fansa

Bisa ga cewar rundunar tsaro, an samu bindigogi 296 da kuma harsasai 7,245, ciki har da AK-47 guda 159, bindigogin gida 54, da bindigogi na zamani 19.

Haka zalika, an kwato harsasai 4,836 kira na musamman, 1,506 kirar NATO, da kuma wasu nau’ukan makamai 28 da harsasai 668.

Sojoji sun kama masu satar danyen mai

A kokarin da sojoji ke yi na dakile satar danyen mai, sun kama mutane 122 da ake zargi da satar man fetur.

Bayan haka, sojojin sun kwato lita 1,790,934 na danyen mai da aka sata, lita 402,936 na dizil da aka tace ba bisa ka’ida ba, da kuma lita 600 na man jirgi (DPK).

Hedikwatar Tsaro ta ce za a ci gaba da kai hare-hare kan masu tada zaune tsaye a Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Sojoji
Yadda sojoji suka ceto mutane a hannun 'yan ta'adda. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Al-umma sun yaba da kokarin da sojojin Najeriya ke yi na tabbatar da tsaro a fadin kasar nan tare da rokon Allah ya cigaba da ba su nasara.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ritsa 'yan bindiga a maboyarsu, an kama 'yan ta'adda 20

An kama yan ta'adda 20 a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kai hari wata maboyar 'yan ta'adda a jihar Taraba da ke Arewacin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa yayin farmakin, 'yan sanda sun kama 'yan bindiga 20 tare da kwato tarin makamai a tattare da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng