Fitinannen Dan Ta'addan da Ya Addabi Zamfara, Nabamamu Ya Fada Tarkon Sojoji

Fitinannen Dan Ta'addan da Ya Addabi Zamfara, Nabamamu Ya Fada Tarkon Sojoji

  • Rundunar sojojin kasar nan ta samu nasarar damke wani kasurgurmin dan ta'adda, Kachallah Hassan Nabamamu wanda ya addabi Zamfara
  • Rahotanni sun bayyana cewa bayan cafke shi, yaransa da wasu manyan 'yan ta'adda sun farmaki kauyuka da dama don neman a sake shi
  • Sai dai rundunar ta bayyana cewa ba za ta lamunci wani dan ta'adda ya yi kokarin haramta wa jama'a zaman lafiya a sassan jihar ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Dakarun Sojojin Najeriya na Operation fansan yamma sun cafke fitinannen dan ta'adda, Kachallah Hassan Nabamamu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Nabamamu ya jefa mazauna Mada, Tsafe, da wasu yankunan Jihar Zamfara a cikin tashin hankali da masifa babba.

Zagazola Makama
An cafke fitinannen dan ta'adda Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Zagazola Makama ya ruwaito cewa an kama shi ne a samamen ya gudana a ranar 27 ga Fabrairu 2025 a Hegin Mahe, Ruwan Bore, da ke cikin garin Mada a jihar.

Kara karanta wannan

Dakaru sun yi dirar mikiya a kan 'yan ta'adda ana tsaka da karbar kudin fansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji ‘yan ta’adda

Dakarun sojoji sun kaddamar da kwanton-bauna, wanda ya kai ga musayar wuta mai zafi a tsakanisu da mayakan Nabamamu.

A yayin harin, an kashe ‘yan bindiga da dama, yayin da wasu suka tsere da munanan raunuka, lamarin da ya kara raunata dabar 'yan ta'addan.

Da fari, Nabamamu ya yi kokarin tserewa ta shiga wasu gidajen da ke kusa, amma jami’an tsaro sun bi sawunsa har suka cafke shi da ransa.

‘Yan ta’adda sun kai hari domin daukar fansa

Awanni bayan cafke shi, mabiyan Nabamamu a karkashin jagorancin Bakin Malam sun kai farmaki kan garuruwan Chediya, Bamamu, da Makera.

Sun kai harin domin razana mazauna yankunan, inda suka yi barazanar korar mazauna yankin idan har ba a saki Nabamamu ba.

Zagazola Makama ya ruwaito cewa:

"Har yanzu mutane da dama sun tsere daga gidajensu saboda tsoron harin ramuwar gayya. Sai dai, dakarun Najeriya sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka fatattaki ‘yan bindigan tare da hana su sake tayar da zaune tsaye."

Kara karanta wannan

APC ta fadi abin da zai mayar da Tinubu kujerarsa bayan zaben 2027

An tura karin sojoji a Zamfara

An tura karin dakaru na sama da kasa domin tabbatar da tsaron yankin da hana sake aukuwar irin wannan hari.

Haka kuma, ana ci gaba da gudanar da ayyukan leken asiri domin bankado maboyar ‘yan bindigan da suka tsere.

Yadda yan ta'adda suka addabi Zamfara

Kachallah Hassan Nabamamu wanda aka haifa a Tsafe, Gidan Alhaji Kaduna, kuma ya fara aiwatar da manyan laifuffuka bayan ya shekara 30 da haihuwa.

Zagazola Makama
Fitinannen dan ta'adda a Zamfara Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Facebook

Nabamamu yana aiki tare da wasu fitattun shugabannin ‘yan bindiga kamar su Bakin Malam, Kachallah Mal Tukur, da Kachallah Baldu, tare da jagorantar akalla mayaka 100 da ke dauke da manyan makamai.

'Dan ta'ddan ya tilasta wa kauyukan da ke cikin karamar hukumar Tsafe biyan haraji da ya kai miliyoyin Naira, bayan sace daruruwan mutane.

Sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda

A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun hadin gwiwa sun yi wa wasu 'yan ta'adda kofar rago a lokacin da su ke kokarin musayar wanda suka yi garkuwa da shi da kudin fansa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an tsaron sun samu labarin cewa yan ta'addan sun shirya karfar kudin fansa, lamarin da ya sa aka yi kyakkaywan shiri domin tarwatsa 'yan ta'addan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.