Shugaban EFCC Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Dalilin Karuwar Cin Hanci a Najeriya

Shugaban EFCC Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Dalilin Karuwar Cin Hanci a Najeriya

  • Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya, ya koka kan yadda ƴan Najeriya suke kallon harkokin mulki
  • Olanipekun Olukoyede ya bayyana cewa ƴan Najeriya na ɗaukar shugabanci a matsayin hanyar tara dukiya
  • Shugaban na EFCC ya yi kira ga ƴan Najeriya da su daina goyon bayan mutanen da ake bincika kan zargin karɓar rashawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ola Olukayode, ya yi magana kan matsalar cin hanci a Najeriya.

Olanipekun Olukoyede ya bayyana cewa ƴan Najeriya na yi wa shugabanci kallon wata hanya ta tara dukiya.

Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede
Olukoyede ya koka kan cin hanci da rashawa a Najeriya Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Shugaban EFCC ya halarci taro kan cin hanci

Shugaban na EFCC ya yi magana ne a wurin wani taro kan yaƙi da cin hanci da rashawa a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya fallasa yan siyasa da suka ba shi cin hancin N500m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa, shugaban na EFCC ya jaddada muhimmancin amana da bin ƙa'idoji wajen gudanar da mulki.

Ya bayyana cewa amana tana da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da cin hanci a Najeriya. Ya kuma buƙaci shugabanni da waɗanda suke mulka su gyara halayensu.

Olukoyede ya koka kan halin ƴan Najeriya

Olukoyede ya jaddada cewa bai kamata a ɗauki shugabanci a matsayin wata dama ta tara dukiya ba.

Shugaban na EFCC ya buƙaci a hada kai don yaƙi da cin hanci, yana mai bayyana cewa nasarar wannan yaƙi ya dogara ne da haɗin kan shugabanni da al'umma baki ɗaya.

Ya shawarci jama'a da su guji kare waɗanda ake bincika kan cin hanci, maimakon haka, su marawa ƙoƙarin hukumar na bincike da hukunta irin waɗannan mutanen baya.

"Ina ci gaba da faɗawa mutane cewa shugabanci aiki ne mai matuƙar nauyi. Shugabanci shi ne aiki mafi wahala a duniya, musamman a wuraren da abubuwa ke tafiya yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

"Abin takaici, a nan ana ɗaukar shugabanci a matsayin hanyar tara dukiya, shi ya sa cin hanci da rashawa ya yi ƙamari sosai."
“Ba na nufin cewa ni waliyyi ne. Abin da nake cewa shi ne, akwai wasu abubuwa da ya kamata ka gujewa idan ka samu kanka a irin wannan matsayi mai haɗari da muke ciki. Domin idan kana yaƙi da cin hanci, babu wanda zai iya kama ka da wani abu."

- Ola Olukoyede

Shugaban EFCC ya ba da shawara

Ya ƙara da cewa yaki da cin hanci aiki ne da yake kan wuyan kowa da kowa.

"Idan ka ga ana binciken mutane kuma an gabatar da hujjoji, kada ka goyi bayansu wajen zagin EFCC, ICPC da sauransu, domin hakan na taimakawa matsalar cin hanci ta ci gaba."
“Ka tsaya ka tambayi kanka, shin za ka iya kare duk abin da kake da shi a halin yanzu bisa gaskiya? Har yanzu akwai mutanen kirki masu gaskiya a wannan ƙasa. Mu ba su goyon baya."

- Ola Olukoyede

An buƙaci EFCC ta cafke El-Rufai

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Tinubu ya fadi kudaden da ake ba gwamnonin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Kiristocin Arewa ta buƙaci hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Ƙungiyar ta buƙaci hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta cafke El-Rufai ne kan zargin yin sama da faɗi da Naira biliyan 423 lokacin da yake mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng