Gwamna Abba Ya Fusata kan Yankewa Ma'aikata Albashi, Ya Dauki Mataki
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bai ji daɗin rahotannin da ke cewa ana yankewa wasu ma'aikata albashinsu ba
- Abba Yusuf ya bayyana hakan a matsayin cin zali da take haƙƙin ma'aikatan da ke fafutuka domin neman na kansu
- Gwamnan ya kafa kwamitin bincike da nufin bankaɗo masu hannu a aika-aikar domin su fuskanci hukuncin da ya dace da su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana da kakkausar murya kan rage albashi da kuma rashin biyan wasu ma’aikatan gwamnati haƙƙoƙinsu.
Gwamna Abba ya bayyana hakan a matsayin take haƙƙin ma'aikata da kuma cin amanar jama’a.

Asali: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
El Rufa'i ya fadi yadda aikin Ribadu ke taimaka wa 'yan ta'adda da miyagun makamai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya kaɗu kan yanke albashin ma'aikata
Gwamna Abba Kabir ya fusata da bayanan da ke nuna cewa wasu ma’aikata sun shafe watanni ba tare da an biya su haƙƙoƙinsu ba.
Gwamnan ya sha alwashin banƙado masu hannu a wannan ɗanyen aikin tare da hukunta su.
“Wannan gwamnatin ba za ta amince da wani nau’i na zalunci ga ma’aikatanmu ba. Duk wanda aka kama da hannu a wannan aika-aika zai fuskanci hukunci mai tsanani."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Wane mataki gwamnan Kano ya ɗauka?
A ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen waɗannan matsalolin, gwamnan ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi domin gudanar da bincike kan asalin matsalar.
An ba da umarni ga kwamitin da ya gudanar da bincike kan tsarin biyan albashi na jihar daga watan Oktoba 2024 zuwa Fabrairun 2025.
Kwamitin zai gano ma’aikatan da abin ya shafa, tantance asarar da aka tafka, tare da bayar da shawarwari kan matakan da ya kamata a ɗauka don gyarawa da hukunta masu laifi.
Kwamitin yana da mambobi bakwai ƙarƙashin jagorancin Hon. Abdulkadir Abdussalam, kwamishinan harkokin karkara da ci gaban al’umma, kuma tsohon Akanta Janar na jihar Kano.
Kwamitin ya ƙunshi manyan jami’an gwamnati da ƙwararru a harkar kudi da tsarin biyan albashi.
Ga jerin sunayen mambobin kwamitin:
- Hon. Abdulkadir Abdussalam - Shugaban Kwamitin
- Dr. Bashir Abdu Muzakkari - Mamba
- Dr. Aliyu Isa Aliyu - Mamba
- Dr. Hamisu Sadi Ali - Mamba
- Hajiya Zainab Abdulkadir - Mamba
- Aliyu Muhammad Sani - Sakataren kwamitin
- Ummulkulthum Ladan Kailani - Sakatariya ta biyu
An ba kwamitin bincike wa'adi
An bai wa kwamitin wa’adin kwanaki bakwai domin kammala bincike tare da gabatar da cikakken rahoto kan waɗanda ke da alhakin aikata laifin, yawan kudin da aka salwantar, da matakan da za a ɗauka don hana sake faruwar irin haka.
Abba ya tabbatar wa ma’aikatan gwamnati cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare hakkinsu, yin adalci, da tabbatar da biyan albashi akan kari,

Kara karanta wannan
"Mun inganta tsaro," Shugaba Tinubu ya yi magana bayan El Rufai ya faɗi maganganu
Ya jaddada cewa duk wanda aka kama yana cin zalin ma’aikata zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Gwamnatin Abba za ta gina makarantu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano, za ta gina sababbin makarantu domin inganta ilmin mata na tsarin AGILE.
Sababbin makarantun da gwamnatin za ta gina sun ƙunshi, ƙananan sakandare guda 75 da manyan makarantun sakandare 55 a sassa daban-daban na jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng