Rigima kan Wa'azin Ramadan a Masallacin Juma'a Ta Yi Tsami, Kotu Ta Shiga Tsakani

Rigima kan Wa'azin Ramadan a Masallacin Juma'a Ta Yi Tsami, Kotu Ta Shiga Tsakani

  • Babbar Kotun Tarayya a Lagos ta yi zama kan rikici da ake yi game da wa'azin watan Ramadan a babban masallacin jihar
  • Kotun ta umarci bangarorin da ke rikici kan wa’azin Ramadan a babban masallacin su kiyaye doka tare da zaman lafiya
  • Mai shari’a, Ambros Lewis-Alagoa ya ce tun da babu gardama kan shugabanci, jagorancin babban limamin masallacin zai ci gaba da shirya wa’azin Ramadan
  • Rikicin ya samo asali ne daga takaddama tsakanin Sheikh Sulaimon Abou-Nolla da Alhaji Sikiru MacFoy kan nadin Baba Adinni da tafiyar da harkokin masallacin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - A yayin da rikicin babban masallacin Juma'a na Lagos ke ci gaba da ruruwa, Babbar Kotun Tarayya a jihar ta ba da umarni kan takaddamar.

Kotun ta umarci dukkan bangarorin da ke rikici kan wa'azin watan Ramadan su dakata.

Kara karanta wannan

Mai alfarma sarkin musulmi ya aika saƙo ga malamai ana shirin fara azumin Ramadan

Kotu ta shiga tsakani kan rigima a masallacin Juma'a a Lagos
Kotu ta bukaci dukkan bangarorin da ke rigima kan masallacin Juma'a a Lagos da su bi umarninta. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda rigima ta jawo rufe masallacin Juma'a

Daily Trust ta ce kotun ta bukaci wadanda abin ya shafa su guji duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali a jihar, tare da kiyaye doka da oda.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Legas ta rufe masallacin Hausawa saboda rikicin shugabanci da ya barke bayan rasuwar babban limamin masallacin.

Bangarori uku ne ke takara kan limancin; wanda ya hada da iyalan mamacin, bangaren Sarkin Hausawan Agege, da na Na'ibi wanda ke ikirarin shi ya dace.

Shugaban karamar hukumar Agege karkashin jagorancin Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi ya ce rufe masallacin na wucin gadi ne, kuma za a yi zama don sulhunta bangarorin da ke rikicin da neman hanyar kawo karshen lamarin.

Rikicin limancin a masallacin ya barke ne tun bayan rasuwar babban limamin Hausawa na Agege, Sheikh Sharif Habib Abdul-Majid, a tsakiyar watan Janariun 2025.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi domin cin moriyar watan Ramadan

Kotu ta umarci bin doka da oda kan rigimar da ake yi a masallacin Juma'a

Source: Facebook

Wane umarni Kotu ta bayar kan rigimar masallacin?

Mai shari’a, Ambros Lewis-Alagoa ya bayyana cewa babu gardama kan shugabanci a masallacin, kamar yadda rahoton The Nation ya tabbatar.

Don haka, babban limamin masallacin, wanda ke da jagorancin addini, shi ne zai ci gaba da shirya wa’azin Ramadan har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan dambarwar da ke neman sauya salo.

Wannan umarni na kotu ya biyo bayan shari’ar da kungiyar Musulunci da Alhaji Femi Okunnu, da Alhaji Cif Saheed Yemi Lawal suka shigar.

Daga bisani, alkalin kotun ya tabbatar da dage sauraron karar zuwa wani lokaci wanda ba a bayyana ba.

Kano: DSS ta gayyaci Sheikh Bin Uthman

A wani labarin, kun ji cewa bayan masallacin Juma'a a Kano ya dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga jagorantar sallah, hukumar DSS ta gayyace shi domin amsa wasu yan tambayoyi.

Ana zargin hudubar da Bin Uthman ya gabatar ta jawo fushin jama’a, har ta kai ga kusan afkawa sakataren kwamitin amintattun masallacin wanda malamin ya dade yana jagoranta.

Kara karanta wannan

Mubarak Bala da ƴan Arewa 4 da aka taɓa yankewa hukuncin kisa kan ɓatanci ga Annabi

Hukumar tsaro ta farin kaya ta gargadi Bin Uthman da gujewa hudubobi masu tayar da hankali, yayin da majalisar malamai ta ba shi shawara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.