'Yan Sanda Sun Ritsa 'Yan Bindiga a Maboyarsu, an Kama 'Yan Ta'adda 20
- Rundunar ‘yan sanda a Taraba ta kama mutum 20 tare da kwato makamai da alburusai a wani samame da ta kai
- Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne a gonakin shinkafa na Wamunchi, bayan samun sahihan bayanan sirri
- Sufeto Janar na ‘yan sanda ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin tare da alkawarta kare rayuka da dukiyoyin jama’a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mutum 20 da ake zargi da aikata laifuffuka tare da kwato makamai a wani samame da suka kai a jihar Taraba.
An kai wannan farmaki ne ranar Talata, 26 ga watan Fabrairu, 2025, a gonakin shinkafa na Wamunchi, bisa bayanan sirri da aka samu daga hukumomin tsaro.

Asali: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa rundunar ‘yan sandan ta ce ta kwato mugayen makamai da suka hada da bindiga AK-47, alburusai, bindigogi kirar gida da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun kama 'yan bindiga 20
Jami’an tsaro sun kai farmakin bisa ga umarnin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Taraba, bayan samun sahihan bayanai kan maboyar ‘yan bindiga a yankin.
A yayin farmakin, jami’an sun yi nasarar cafke mutum 20, dukkansu maza, wadanda ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban a jihar.
Bayan cafke su, an wuce da su domin gudanar da bincike na musamman a sashen binciken manyan laifuffuka na jihar (SCID), domin gano hakikanin laifukan da suka aikata.
Rundunar ‘yan sandan ta ce za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
An kwato makamai da wasu kayayyaki
Bayan kama masu laifin, jami’an tsaro sun kuma kwato makamai da wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen aikata laifuffuka a yankin.
Kayan da aka samu sun hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, alburusai bakwai, bindigogi kirar gida guda uku, kwari da baka da kuma babur guda daya da ake amfani da shi wajen ta'addanci.
‘Yan sanda sun bayyana cewa makaman da aka kwato sun nuna irin hadarin da wadannan gungun ‘yan ta’adda ke haifarwa a jihar Taraba da kewaye.
Haka kuma, an bukaci al’ummar yankin da su rika bayar da bayanai ga jami’an tsaro domin dakile ayyukan miyagun mutane.

Asali: Facebook
Sufeto janar ya yabi jami'an 'yan sanda
Sufeto Janar na ‘yan sanda ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai cewa rundunar na ci gaba da aiki tukuru domin ganin an kakkabe duk wata maboyar ‘yan ta’adda.
Ya kuma tabbatar wa da al’ummar jihar Taraba cewa za su ci gaba da ganin daukar matakai na tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun yi dirar mikiya kan 'yan ta'adda, sun kashe miyagu 2, an kama 3
Mutanen gari sun kama 'yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen gari sun yi kukan kura sun kama wasu 'yan bindiga da suka kai hari jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa jama'ar garin sun hallaka 'yan bindigar bayan kama su da ransu a wani hari da suka yi niyyar kai wa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng