Matatar Ɗangote Ta Jefa Ƴan Kasuwa a Matsala da Ta Rage Farashin Fetur Ana Shirin Ramadan

Matatar Ɗangote Ta Jefa Ƴan Kasuwa a Matsala da Ta Rage Farashin Fetur Ana Shirin Ramadan

  • Dillalan mai da ke shigo da kaya daga ƙasashen ketare sun koka kan rage farashin fetur da matatar Ɗangote ta ƙara yi a Najeriya
  • Ƴan kasuwar sun bayyana cewa wannan ragin da aka yi zai jefa kasuwancin su cikin matsala kuma da yiwuwar su yi asara
  • A jiya Laraba matatar Ɗangote ta sanar da rage farashin kowace lita daga N890 zuwa N825 kuma matakin zai fara aiki yau Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Manyan ƴan kasuwa da ke shigo da man fetur sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da rage farashin man fetur da Matatar Dangote ke yi a kasuwa.

Wasu daga cikin masu shigo da man sun ce hakan na iya tilasta su sayar da hajarsu a farashin da babu riba, domin masu sayen mai za su fi saye daga inda ya fi araha.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashin man fetur, an fara maganar karya farashin siminti a Najeriya

Gidan mai.
Yan kasuwa masu shigo da mai sun koka kan rage farashin man fetur Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ɗangote ya rage farashin man fetur

Punch ta tattaro cewa a ranar Laraba, Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga N890 zuwa N825 a kowace lita, wanda zai fara aiki daga yau, 27 ga Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ne karo na biyu da aka rage farashin man a cikin sabuwar shekara watau 2025 kuma karo na uku cikin wata biyu.

Duk da cewa shigo da man fetur daga waje ya ragu, akwai dillalai da har yanzu ke shigo da shi daga kasashen ketare, rahoton Channels tv.

Hukumar kula da harkokin mai (NMDPRA) ta tabbatar da cewa kusan kashi 50 cikin 100 na mai da ake amfani da shi a cikin gida har yanzu ana shigo da shi daga waje.

Sai dai yayin da ‘yan Najeriya ke murna da rage farashin, masu shigo da man fetur sun fara jin illar hakan ga kasuwancinsu.

Rage farashin fetur bai yi wa wasu daɗi ba

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Wasu dillalai sun ce matatar Dangote na rage farashi ne don hana shigo da mai daga kasashen waje, kuma hakan na tilasta wa ƴan kasuwa siyar da kayansu da riba kadan ko asara.

Wani dillali da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce:

"Wasu daga cikinmu da muka shigo da mai muna jin radadin wannan mataki. Duk da cewa rage farashin abu ne mai kyau ga jama’a, mu illa ce a kasuwancin mu."

Wani mai sayar da mai ya ce, “Yadda matatar Dangote ke rage farashin mai da dizal zai sa mutane da yawa su daina shigo da shi daga waje.”

Masu shigo da mai na iya yin asara – IPMAN

A wata hira, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya ce wannan matakin na iya jefa masu shigo da mai cikin asara.

“Dangote na iya murƙushe shigo da mai idan har ya ci gaba da rage farashi kowace lita.

Kara karanta wannan

Ramadan: Yadda kayan abinci suka yi sauki a Arewa ana shirin azumi

"Wadanda suka nemi kalubalantar Dangote da cewa za su shigo da fetur mai araha, kafin su iso bakin teku, Dangote ya sake rage farashin, wanda hakan zai jefa su cikin matsala.

Ana fargabar karancin fetur a Legas

Kun ji cewa direbobin tankokin dakon mai sun dakatar da ayyukansu a jihar Legas da wasu jihohi, hakan ya sa ake fargabara ƙarancin man fetur.

A cewar direbobin, sun ɗauki wannan matakin ne domin nun ɓacin ransu kan cin zarafin da ake yi masu a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262