Zuwan Hafsan Sojoji Ya Kawo Alheri, Ya Yi wa Dakaru Albashir bayan Kara Alawus

Zuwan Hafsan Sojoji Ya Kawo Alheri, Ya Yi wa Dakaru Albashir bayan Kara Alawus

  • Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya ƙara kuɗin ciyarwa na sojoji daga N1,500 zuwa N3,000 a kullum
  • Oluyede ya kuma bayyana cewa an kaddamar da shirin gidaje don ba wa sojojin da ke ritaya wuraren zama
  • An ƙaddamar da rancen sojoji da riba kashi 3% kawai, wanda ya fi sauƙi fiye da na bankuna wanda sojoji za su iya samun kayayyakin aiki da sauri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-janar Olufemi Oluyede, ya yi albashir ga sojojin Najeriya da ke bakin aiki.

Laftanar-janar Oluyede ya sanar da ƙarin kuɗin alawus na abincin sojojin Najeriya daga N1,500 zuwa N3,000, farawa daga ƙarshen Maris din 2025.

An kara wa sojoji alawus na abinci domin inganta ayyukansu
Hafsan sojoji, Laftanar-janar Olufemi Oluyede ya yi wa rundunar alkawarin inganta walwalarsu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Oluyede ya shiga damuwa kan walwalar sojoji

Oluyede ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga jami'ai da sojojin Rundunar 81 a Filin Taron 9th Brigade da ke Ikeja, Lagos, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashin man fetur, an fara maganar karya farashin siminti a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hafsan sojojin ya nuna takaicinsa cewa har yanzu ana biyan sojoji N1,500 a matsayin kuɗin ciyarwa, ya tabbatar da cewa yana da niyyar inganta jin daɗin su.

Ya kuma ambaci matsalar gidaje da ke damun jami'an masu aiki, inda da yawa ba su da gidajen da za su koma bayan ritaya.

Don magance matsalar, Oluyede ya bayyana cewa Sojojin Najeriya sun ƙaddamar da shirin gidaje don bai wa sojojin da ke ritaya wuraren zama.

Shugaban sojoji ya yi karin alawus na abincin jami'ansa

Hafsan sojoji ya yi alkawarin inganta jami'ansa

A cewarsa:

"Ina shirin inganta abin da magabata na suka yi don kyautata jin daɗin jami'anmu, a watan Disamba, mun ƙaddamar da gidaje na farko a Abuja.
"Yanzu mun fara sababbi a Ibadan, mun samu fili a Jos, hakanan, muna gina gidaje a Fatakwal, Owerri, da Akwa Ibom."

Sannan ya ƙara da cewa shirin zai bai wa sojoji gidaje masu rahusa, yana mai cewa babu inda za a samu gida mai ɗaki biyu ko uku kan N8m, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya faɗo kan gidajen mutane, Janar da wasu sama da 40 sun mutu

Ya ce:

"Wannan zai tabbatar da cewa an rarraba gidaje ga sojoji. Ku sani babu inda za a samu gida mai ɗaki biyu ko uku kan N8m.
"Wannan babbar gudunmawa ce daga Sojoji don tabbatar da cewa kuna da kyakkyawar rayuwa bayan ritaya. Muna hanzarta aikin don yawancin sojoji su amfana."

Oluyede ya ba sojoji tabbacin kayan aiki

Game da matsalar siyan kayan sojoji, Oluyede ya tabbatar musu cewa an fara rabon kayan aiki N100,000 a kowane wata.

Hafsun ya amince da wahalar samun kayan aiki, amma ya tabbatar wa sojoji cewa ana kokarin samar musu da abin da suka bukata.

Oluyede ya kuma bukaci sojojin da su ci gaba da jajircewa, yana mai cewa ƙoƙarinsu yana da matuƙar muhimmanci ga nasarar Sojin Najeriya.

An shawarci yan Najeriya kan murkushe yan ta'adda

Kun ji cewa wata kungiyar matasa a Arewacin Najeriya ta fadi rawar da al'umma za su taka wurin ganin an kakkabe yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Abin da sojoji ke bukata daga al'ummar Najeriya domin murkushe Bello Turji'

Kungiyar NWYPD ta bukaci hadin kan jama’a don tallafawa sojoji a kokarinsu na yakar Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.