An Shiga Jimami bayan 'Yan Sanda Sun Rasu yayin Artabu da 'Yan Bindiga
- Jami'an ƴan sandan Najeriya sun samu nasarar daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane da ƴan bindiga suka yi a jihar Plateau
- Ƴan sandan sun fatattaki ƴan bindigan waɗanda suka so yin awon gaba da mutane a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu ta jihar
- Sai dai, abin ban takaici, wasu jami'an ƴan sanda guda biyu sun rasa rayukansu yayin artabun da suka yi da miyagun ƴan bindigan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe jami’an ƴan sanda biyu a jihar Plateau.
Ƴan bindigan sun kashe ƴan sandan ne a lokacin da suka yi ƙoƙarin yin garkuwa da wasu mutane a yankin Little Rayfield da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau.

Asali: Twitter
Ƴan sanda sun tabbatar da lamarin
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Plateau, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Jos, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DSP Alabo Alfred ya bayyana cewa an kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a yunƙurin satar mutanen, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Ƴan bindiga sun so sace mutane
Wasu mazauna yankin Little Rayfield sun bayyana cewa misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Talata, sun ji harbe-harbe a yankin.
Sun bayyana cewa masu garkuwan sun yi ƙoƙarin sace wasu mutane, amma jami’an ƴan sanda sun dakile shirin nasu.
A cewar DSP Alfred, jami’an ƴan sandan da aka kashe, sun zo wani aiki ne na musamman a jihar daga hedikwatar rundunar ƴan sanda da ke Abuja.
Ƴan sanda sun faɗi abin da ya faru
"Rundunar ƴan sandan jihar Plateau na son sanar da jama’a cewa an kama mutum huɗu da ake zargi da yunƙurin garkuwa da mutane a yankin Little Rayfield da ke Jos."
“Sai dai, biyu daga cikin jami’anmu, wato Fatoyo Femi da Dafur Dashit, waɗanda ke aiki a sashen bincike na musamman na rundunar ƴan sanda da ke Abuja (IRT), sun rasa rayukansu a yayin musayar wuta da masu garkuwa da mutanen."
"A halin yanzu, ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma za a sanar da al’umma ƙarin da bayani daga baya."
"Kwamishinan ƴan sandan jihar Plateau, CP Emmanuel Olugbemiga Adesina, yana kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu, domin an ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro."
- DSP Alabo Alfred
Sojoji sun daƙile harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji masu aikin wanzar da zaman lafiya sun samu nasara kan 'yan bindiga a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Jami'an tsaron sun kai ɗaukin gaggawa ne bayan sun samu rahoton cewa ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen a tsakar dare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng