‘Abin da Sojoji Ke Bukata daga Al’ummar Najeriya domin Murkushe Bello Turji’
- Kungiyar NWYPD ta bukaci hadin kan jama’a don tallafawa sojoji a kokarinsu na yakar Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma
- Shugaban kungiyar, Salihu Bello ya yabawa kokarin sojoji wajen dakile ayyukan ‘yan bindiga, yana mai cewa lallai jama’a su nuna godiya da goyon baya
- Bello ya ce dole ne a yi nazari kan wadanda ke goyon bayan ‘yan ta’adda kai tsaye ko a boye, domin wanzar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma
- Wannan na zuwa ne yayin da sojoji suka kara kaimi wurin tabbatar da kawo karshen yan ta'adda da suka addabi al'umma a Arewacin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar North-West Youths for Peace and Development, NWYPD, ta shawarci al'umma kan yaki da ta'addanci a yankin.
Kungiyar ta bukaci hadin kan jama’a wajen tallafawa sojojin Najeriya a yakin da suke yi da Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda.

Asali: Facebook
Sojoji sun sha alwashin kawo karshen Turji
Daily Nigerian ta ce Shugaban kungiyar, Salihu Bello ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Tarayya, Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan sojoji sun ce karshen ta'addancin hatsabibin ɗan bindiga Bello Turji, ya kusa zuwa bayan sun gano inda yake.
Rundunar sojoji ta ba da tabbacin nan ba da jimawa ba za a kawar da Bello Turji wanda ya addabi mutanen Zamfara da sauran jihohin makwabta.
Sojojin sun buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri domin bibiyar hatsabibin ɗan bindiga aiki ne mai wahalar gaske.

Kungiya ta nemo dabarar kama Bello Turji
Salihu Bello ya ce dole ne mutane su fahimci irin kokarin da sojojin Najeriya ke yi domin tabbatar da zaman lafiya.
A cewarsa:
“Sojoji na bukatar goyon bayanmu don dawo da zaman lafiya a Arewa maso Yamma da sauran yankuna.
“Yayin da muke kokarin ci gaban tattalin arzikin yankinmu, wasu suna hana ci gaba. Abin takaici, mutanenmu ne ke aikata hakan.”
Salihu Bello ya ce bukaci a binciki wadanda ke tallafawa ‘yan bindiga kai tsaye ko a boye, Peoples Gazette ta ruwaito.
Ya ce:
“Ta yaya muka zo wannan hali? Su wanene ke marawa wadannan mutane baya da daukar nauyinsu?.
“Muna kira ga mutanenmu da su ci gaba da bayar da goyon baya ga sojoji don samun zaman lafiya."
Shugaban kungiyar ya kuma yabawa shugabancin Janar Christopher Musa kan namijin kokarin da sojoji ke yi.
Bello Turji: Sojoji sun ba al'umma umarni
Kun ji cewa bayan Bello Turji ya kakabawa wasu mazauna yankuna biyan N25m, rundunar sojoji ta ba su umarni.
Rundunar soji ta bukaci al’ummomi da su yi watsi da bukatar biyan kudi ga ‘yan bindiga, domin sojoji na aiki don tabbatar da tsaronsu.

Kara karanta wannan
Karya ta kare: Sojoji sun gano maboyar Bello Turji, sun fadi lokacin kawar da shi
Manjo-janar Onumajuru ya ce Turji ya tsere tun bayan farmakin da sojoji suka kai masa a Zamfara, kuma ana bin sawunsa don kashe shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng