Sabuwar Zanga Zanga ta Barke a Kano, An Samu Bayanai

Sabuwar Zanga Zanga ta Barke a Kano, An Samu Bayanai

  • Wata sabuwar zanga-zanga ta ɓarke a cikin birnin Kano a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairun 2025
  • Zanga-zangar wacce ba a bayyana musabbabin gudanar da ita ba, ta ɓarke ne a Ƙofar Nasarawa da ke cikin birnin Kano
  • Jami'an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda, DSS sun ɗauki matakin tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar sanya musu barkonon tsohuwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - An samu ɓarkewar zanga-zanga a cikin birnin Kano a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairun 2025.

Zanga-zangar ta auku ne a ƙarƙashin gadar ƙofar Nasarawa da ke cikin birnin Kano.

Zanga-zanga ta barke a Kano
Mutane sun yi zanga-zanga a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa jami’an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da DSS sun tarwatsa masu zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga ta ɓarke a birnin Kano

Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun yi dandazo a ƙarƙashin gadar Ƙofar Nasarawa, da ke cikin birnin Kano.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga, sun yi raga raga da miyagu

Sai dai, jami’an tsaro sun yi gaggawar zuwa wurin inda suka yi musu tarnaƙi da barkonon tsohuwa.

Har yanzu dai ba a gano musabbabin gudanar da zanga-zangar a cikin birnin na Kano ba.

Sai dai tuni jami’an tsaro suka ɗauki matakin sanya shamaki a hanyoyin da ke daura da zuwa Gidan Gwamnatin Kano.

Me ƴan sanda suka ce kan zanga-zangar?

Jami'in hulɗa da jama'a na ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.

Ya ce ƙura ta lafa kuma kawo yanzu sun cafke mutum 17 da ake zargin suna da hannu a gudanar da zanga-zangar.

"Rundunar ƴan sandan jihar Kano na son sanar da jama’a cewa an ɗauki ingantattun matakan tsaro domin hana karya doka da oda a cikin jihar."
"Bisa ga sahihan rahotannin sirri da ke nuna shirin gudanar zanga-zanga da wasu mutane ke yi, rundunar, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ta tura jami’ai da kayayyakin aiki zuwa wurare a cikin birnin Kano domin tabbatar da tsaron al’umma."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hada mutane da dabbobi sun yi gaba da su a jihar Neja

"Sakamakon ɗaukar waɗannan matakan gaggawa, an kama mutum 17 da ake zargin ƴan daba ne, kuma ana ci gaba da bincike."
"Rundunar a jajirce take wajen tabbatar da cewa duk waɗanda ke da hannu a wannan shirin zanga-zangar tashin hankalin sun fuskanci hukunci."

- Abdullahi Haruna Kiyawa

An kashe mutum 10 sakamakon zanga-zanga a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa domin bincike kan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da gwamnati, ya gabatar da rahotonsa.

A cikin rahoton da kwamitin binciken ya gabatarwa, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya bayyana cewa mutane 10 sun rasa rayukansu yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata sakamakon zanga-zangar.

Hakazalika, kwamitin ya gano cewa an lalata dukiyar ƴan kasuwa da kadarorin gwamnati a lokacin zanga-zangar.

Gwamn Abba Kabir Yusuf ya ɗauki alƙawarin aiwatar da dukkanin shawarwarin da kwamitin ya gabatar masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng