'Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Jami'ar Tarayya, Sun Bar Ɗalibai cikin Firgici
- Ɗalibai sun shiga tsahin hankali da wasu ƴan bindiga suka kai hari jami'ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurɗi a jihar Benuwai
- Majiyoyi daga jami'ar sun bayyana cewa maharan sun ce ɗalibai huɗu da suka fito karatu kuma har yanzu babu wani labarinsu
- Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sanda, Sewuese Anene ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ɗalibai biyu aka sace ba huɗu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Ƴan bindiga sun sace dalibai mata kusan huɗu a Jami’ar Joseph Sarwuan Tarka, da ke Makurdi a jihar Benue, wacce a baya ake kira da Jami'ar Noma ta Tarayya a daren Talata
Wani dalibi mai suna Ashar Lubem ya faɗawa manema labarai yau Laraba cewa adadin daliban da aka sace hudu ne, kuma lamarin ya jefa sauran daliban cikin firgici.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Asali: Original
Ɗaliban jami'ar sun shiga firgici
Kamar yadda Punch ta tattaro, ɗalibin ya bayyana cewa tun bayan faruwar lamarin, har yanzu ba su ji ɗuriyar ɗaliban da aka yi garkuwa da su ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa lamarin ya jefa ɗalibai da al'ummar makarantar cikin firgici da tsoron abin da ka iya faruwa.
"Wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai hudu a wajen harabar jami’a jiya da yamma. Har yanzu ba mu ji labarinsu ba. A halin yanzu, dukkan dalibai suna cikin tsoro da firgici," in ji Lubem.
Wata majiya ta shaidawa Channels tv cewa duka ɗaliban da aka sace mata a harin mata ne.
“An yi garkuwa da dalibai mata hudu a harabar jami’ar da misalin karfe 8:30 na dare, lamarin da ya haifar da firgici game da lafiyar dalibai."
Ƴan sanda sun tabbatar da sace ɗaliban
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Benue, Sewuese Anene, ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta ce sun samu rahoton cewa dalibai biyu aka sace, ba hudu ba.
"Mun samu labari a yammacin jiya cewa an sace dalibai biyu. Mun fara bincike kuma za mu bayar da karin bayani nan gaba," in ji ta.

Asali: Getty Images
Yadda maharan suka sace ɗaliban jami'a
Wani babban ma’aikacin jami’ar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa daliban suna kan hanyarsu ta zuwa karatu da daddare lokacin da aka sace su.
Ya ce ɗaliban sun fito ne da nufin zuwa yankin North Core da ke kusa da dakunan kwana, kwatsam suka faɗa hannun masu garkuwa da mutame.
Bayan labarin ya bazu, dalibai sun gudanar da zanga-zanga a harabar jami’ar, dauke da rassan bishiya suna bukatar mahukunta su dauki mataki na gaggawa.
Masu zanga-zangar sun bukaci hukumar jami'ar da jami'an tsaro su gaggauta ɗaukar matakin ceto ƴan uwansu da aka sace cikin ƙoshin lafiya.
An sace mataimakin ciyaman a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa ana zargin yan ta'adda sun yi awon gaba da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma da wasu bayin Allah a Zamfara.

Kara karanta wannan
APC ta yi bayani kan ƴan Majalisa 27 da ake zargin sun sauya sheka daga PDP zuwa cikinta
Mazauna yankin sun ce maharan sun yi amfani da motar bas wajen sace mutanen maimakon babura domin kaucewa jami'an tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng