Littafin IBB: Fitaccen Lauya, Falana Zai Maka Janar Babangida a Kotu, Ya Jero Dalilai
- Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya fitar da littafin tarihin rayuwarsa da wasu batutuwa da suka shafi mulkin Najeriya
- A littafin, IBB ya tabbatar da cewa MKO Abiola ne ya lashe zaben 12 ga Yunin 2025 lamarin da ya sa fitaccen lauya ya yanke shawarar shigar da kara
- Femi Falana ya ce a lokacin da ya kalubalanci soke zaben, an kama shi, aka gurfanar da shi a kotu ba bisa ka'ida ba, yana neman hakki
- Lauyan ya ce ya tara tawagar lauyoyi domin kalubalantar Babangida a kotu, yana mai cewa soke zaben ya tauye masa hakkinsa dan Adam
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Fitaccen lauya a Najeriya, Femi Falana zai maka tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida a kotu.
Falana ya bayyana shirinsa na kai karar IBB bayan karanta abubuwan da ke kunshe a cikin littafinsa (A Journey in Service).

Asali: Twitter
IBB ya yi fallasa kan zaben Abiola
Femi Falana SAN ya bayyana haka ne a cikin wata hira da Channels TV a ranar 25 ga Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan tabbatar da cewa MKO Abiola wanda ya lashe zaben 12 ga Yunin 1993 da IBB ya yi da ake ganin a matsayin mafi sahihanci a tarihin Najeriya.
Amma abin mamaki Janar Babangida ya soke sakamakon, yana mai cewa akwai matsaloli a zaben.
Wannan soke zabe ya haddasa zanga-zanga, wanda daga karshe ya kai ga saukar Babangida daga mulki, sai Janar Sani Abacha ya karbi shugabanci.
A yayin gabatar da littafinsa, A Journey in Service, a Abuja a ranar 20 ga Fabrairun 2025, Janar Babangida ya bayyana cewa yana nadamar soke zaben 12 ga Yunin 1993.

Kara karanta wannan
IBB: 'Dalilan kitsa harin rashin imani da ya kashe tsohon shugaban kasa, Murtala'

Abiola: Femi Falana zai maka IBB a kotu
Bayanan IBB a littafin ya tabbatar da matsayar Falana kuma ya sa shi shirin shigar da kara kan cin zarafi da tauye hakki.
Falana ya ce ya kalubalanci soke zaben a lokacin, amma aka kama shi aka gurfanar da shi a kotu. Bayyanar da Babangida ya yi a littafinsa ya kara tabbatar da cewa MKO Abiola ne ya lashe zaben.
Lauyan ya ce yana shirin kai kara kan cin zarafi da tauye masa hakkin dan Adam, duk da cewa lamarin ya faru shekaru 32 da suka gabata, cewar Vanguard.
Falana ya ce:
"Ina shirin kalubalantar kama ni da sauran abokaina ba bisa ka’ida ba, na hada tawagar lauyoyi domin duba lamarin.
"Ya dawo da batun a yanzu, yana mai cewa babu dalilin da ya sa aka kama ni, tun da ya tabbatar cewa MKO Abiola ne ya lashe zaben 12 ga Yunin 1993 wanda muka tsaya tsayin daka a kansa."
Janar IBB ya fadi dalilin hallaka Murtala
Mun ba ku labarin cewa a cikin littafinsa, Janar Ibrahim Babangida ya fadi wasu muhimman batutuwa a kan kisan Janar Murtala Ramat Muhammad.
Janar IBB mai ritaya ya tabbatar da cewa an fara shirin kashe shugaban ne tun daga lokacin da ya karɓi mulkin kasa a shekarar 1975.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng