Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara kan 'Yan Bindiga, Sun Yi Raga Raga da Miyagu
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile wani harin ƴan bindiga a wani ƙauyen jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin na rundunar Operation Fansan Yanma sun yi raga-raga da ƴan bindigan bayan sun samu rahoton harin da suka kai a ƙauyen Tafoki
- Saii dai, duk da fatattakar ƴan bindigan, sun yi awon gaba da wani mutum.guda tare da raunata wasu mutane uku
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma sun samu nasarar daƙile harin ƴan bindiga a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun daƙile wani mummunan harin da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Tafoki, da ke ƙaramar hukumar Faskari.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina
Majiyoyin sirri sun bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, da misalin ƙarfe 7:00 na yamma.
Ƴan bindiga da ake ƙiyasta suna kan babura kusan 100, ɗauke da muggan makamai, sun mamaye ƙauyen inda suka riƙa harbi ba kakkautawa domin tsoratar da mazauna yankin.
Dakarun sojoji sun samu rahoton kai harin, inda suka yi gaggawar kai ɗauki, sannan suka fafata da maharan.
Sojoji sun fatattaki ƴan bindiga
A sakamakon fin ƙarfin da sojojin suka yi wa maharan, ƴan bindigan sun gudu zuwa cikin daji, bayan sun sha luguden wuta daga jami’an tsaro.
Duk da cewa sojojin sun samu nasarar daƙile harin, mutane biyu daga cikin mazauna yankin sun rasa rayukansu.
Waɗanda suka mutu sun haɗa da, Yakubu Mai Inji, mai shekaru 45, Ahmed Yahaya, mai shekaru 25.
Haka kuma, wasu mutane uku sun jikkata, inda aka garzaya da su zuwa babban asibitin Funtua domin samun kulawa.
Bayan haka, yayin da ƴan bindigan ke tserewa, sun yi garkuwa da mutum guda wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba.
Bayan harin, jami’an tsaro sun ƙarfafa matakan tsaro a yankin, domin hana maharan komawa su sake kai wani hari.
Haka nan, ana ci gaba da bincike da sintiri domin gano maboyar ƴan bindigan tare da kuɓutar da mutumin da suka sace.
Mutane na buƙatar ɗauki
Har ila yau, mazauna yankin na cikin fargaba saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga a yankin Faskari, wanda ke fama da matsalar rashin tsaro.
Sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara yawan dakarun sojoji, tare da samar da ingantaccen tsari da zai kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga a yankin gaba ɗaya.
Ƴan bindiga sun kai hari a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a ƙauyen Dakpala na ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Kara karanta wannan
Karya ta kare: Sojoji sun gano maboyar Bello Turji, sun fadi lokacin kawar da shi
Ƴan bindigan waɗanda ke ɗauke da muggan makamai sun yi awon gaba da mutane takwas ciki har da jarirai a harin da suka kai a ƙauyen cikin dare.
Miyagun sun kuma sace shanu sama da guda 115 bayan sun farmaki mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng