'Yan Bindiga Sun Ɓullo da Sabuwar Dabara, Mataimakin Ciyaman Ya Faɗa Tarko a Zamfara
- Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Bukkuyum, Bala Muhammad a kan titin Gusau
- An ruwaito cewa maharan sun sace Bala tare da wasu ma'aikata uku da fasinjoji da dama a hanyarsu ta zuwa garin Gusau
- Wani shaida ya bayyana cewa ya ga lokacin da maharan suka tare mutane, suka tare su a motar da suka zo da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Ana zargin ‘yan bindiga da sace mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Bukkuyum, Bala Muhammad, tare da wasu fasinjoji a kan babban titi a jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun ɓullo da dabarar yin garkuwa da mutane, sun koma amfani da motar bas wajen kai hari maimakon babura.

Asali: Original
Ƴan bindiga sun canza dabara a Zamfara
A cewarsa, ƴan bindiga sun zo da wannan dabara ne domin kauce wa kamun jami’an tsaro da kuma sa idon da al'umma ke yi domin haɗa bayanan sirri, in ji Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa mahara sun sace Bala Muhammad tare da ma’aikatan karamar hukumar guda uku da kuma wasu fasinjoji a ranar Litinin da yamma.
Lamarin ya faru ne a yayin da mataimakin ciyaman na Bukkuyum din da tawagarsa suka kama hanya daga Bukkuyum zuwa Gusau, babban birnin Zamfara.
Yadda aka sace mataimakin ciyaman
Ganau, Haruna Malam, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun tare motar fasinjojin, suka fito da su a daji, sannan suka tilasta musu shiga motarsu da ke ajiye a kusa da hanya.
Wani masassaƙi daga kauyen Gadarmanya a ƙaramar hukumar Anka, Usman Dantsoho, ya tsira daga harin, inda ya ce ya ga maharan suna tuka motarsu tare da wadanda suka sace.
“Ina cikin daji tare da kwandon itacena, ina yanke itace da tattara gungume da na adana, kawai na ji harbin bindiga har sau hudu daga hanyar Anka-Bukkuyum.
“Da sauri na tsere daga wurin da nake, na hau wata bishiya. A nan ne na hango ‘yan bindigar sun tare wata mota, suna kwashe mutanen da ke ciki.”

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Bauchi, ango da yayar amarya sun rasu mintuna 30 kafin ɗaura aure
Mutumin ya ce bayan ya koma gida ne yake samun labarin cewa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Bukkuyum na cikin waɗanda ƴan bindigar suka sace.

Asali: Facebook
Matsalar tsaro a jihar Zamfara
Bukkuyum na daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara, tare da Shinkafi, Maradun, Zurmi, Anka, Talata Mafara, da Tsafe.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Abubakar Sadiq, ba domin bai ɗaga kiran wayar tarho da aka yi masa ba.
Yan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa miyagun ƴan bindiga sun kai munanan hare-hare a yankunan ƙananan hukumomin Gusau da Bukkuyum a jihar Zamfara.
Ƴan ta'adda sun kashe mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba ciki har da kananan yara a sababbik hare-haren da suka kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng