'Yan Bindiga Sun Yi Tabargaza a Abuja kusa da Barikin Sojoji, Sun Sace Mutane
- Rahotanni na nuni da cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane a kusa da barikin sojoji na Sani Abacha a Abuja
- Bayanai sun nuna cewa biyo bayan harin, jami’an tsaro sun gano motoci biyu da aka bari a wurin da lamarin ya faru
- Rundunar ‘yan sandan birnin Abuja ta fara bincike tare da daukar matakan ceto mutanen da 'yan bindigar suka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sanda a Babban Birnin Tarayya (FCT) ta fara bincike kan garkuwa da wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga sun yi kusa da hanyar barikin soji na Abacha a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, da misalin karfe 11:31 na dare.

Asali: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa jami’an tsaro sun gano wasu motocin da aka bari a wurin, lamarin da ke nuna alamun cewa an sace mutanen da ke cikinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’an tsaro sun gano motocin da aka bari
Bayan samun labarin harin, rundunar ‘yan sandan birnin tarayya ta tura tawagar sintiri zuwa wurin domin bincike.
A cewar jami’an tsaro, motocin da aka bari sun hada da wata bakar Toyota Prado mai lamba: Abuja RBC 900 SF, mallakin Hon. Shagala Samuel, da kuma Honda Civic mai lamba: RSH 181 TH.
An bayyana cewa akwai yiwuwar ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutanen da ke cikin motocin, sannan suka tsere zuwa daji.
‘Yan sanda sun fara bincike mai zurfi
Bayan tsananta bincike a yankin da lamarin ya faru, jami’an tsaro sun bazama domin kokarin gano inda aka kai mutanen.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun yi dirar mikiya kan 'yan ta'adda, sun kashe miyagu 2, an kama 3
Rundunar ‘yan sanda ta ce an sa ido sosai a dukkan muhimman hanyoyin shiga da fita a FCT domin hana ‘yan bindigar tserewa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa an kwashe motocin zuwa ofishin ‘yan sanda domin gudanar da karin bincike.
Matakan tsaro sun karfafa a Abuja
A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda ta kara kokari wajen ganin an ceto wadanda aka sace tare da damke wadanda suka aikata aika-aikar.
Bayanai sun nuna cewa sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sanda na aiki tukuru domin gano inda mutanen suke da kuma kamo masu laifin.

Asali: Twitter
Rundunar ta bukaci mazauna Abuja da su kasance masu lura da duk wani motsi da basu fahimta ba, tare da sanar da hukumomin tsaro don daukar mataki cikin gaggawa.
Haka zalika rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa ana daukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a babban birnin kasar.
An kashe 'yan bindiga a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen gari sun yi kukan kura sun kama 'yan bindiga a hannu bayan sun kai hari wani kauye a jihar Katsina.
Matasan sun kashe 'yan bindigar ne bayan jami'an tsaro sun raunata su yayin da suka kawo hari garin a kan babura masu tarin yawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng