'Yan Bindiga Sun Hada Mutane da Dabbobi Sun Yi Gaba da Su a Jihar Neja

'Yan Bindiga Sun Hada Mutane da Dabbobi Sun Yi Gaba da Su a Jihar Neja

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani ƙauyen da ke jihar Neja a yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Dakpala na ƙaramar hukumar Shiroro, suka sace mutane takwas ciki har da jarirai
  • Ƴan bindigan sun kuma sace shanu masu yawa da babura guda biyu a yayin harin ta'addancin da suka kai a ƙauyen na Dakpala

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Dakpala da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙauyen, sun sace mutane takwas tare da yin awon gaba da shanu 115.

'Yan bindiga sun kai hari a Neja
'Yan bindiga sun sace mutane a Neja Hoto: @HQNigerianArmy, @HonBago
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga, sun yi raga raga da miyagu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda aka samu labari, ƴan sandan jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin.

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya faru ne a ranar 24 ga watan Fabrairu da misalin ƙarfe 7:10 na dare, inda maharan masu yawa suka shigo cikin ƙauyen ɗauke da makamai.

Daga cikin waɗanda aka sace akwai, Sale Angwan Kawo, Landa Adamu, Ezolo Hussani, Asabe Daniel da jaririnta, Habiba Salogo da jaririnta, Rabi Hussani, da kuma wasu mutane biyu da har yanzu ba a tabbatar da sunayensu ba.

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Barthlomi Amos, ɗan shekara 38, ya samu nasarar tserewa daga hannun ƴan bindigan, sannan ya koma gida cikin ƙoshin lafiya.

Bayan sace mutanen, ƴan bindigan sun kuma kwashe babura guda biyu ƙirar Honda, mallakin mazauna ƙauyen.

A halin yanzu, jami’an tsaro sun ƙaddamar da aikin ceto domin ganin sun kubutar da mutanen da aka ɗauke da kuma dawo da dabbobin da aka sace.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hare hare a Zamfara, sun tafka barna mai yawa

Ƴan bindiga sun takurawa mutane

Harin da aka kai a ƙauyen Dakpala na ƙara nuna irin ƙalubalen tsaro da yankunan karkara ke fuskanta, musamman a jihar Neja, inda hare-haren ƴan bindiga suka zama ruwan dare.

Mazauna yankin na ci gaba da nuna damuwarsu kan yawaitar hare-haren, inda suke kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki ƙarin matakai don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Hare-haren ƴan bindiga a yankunan karkara na ci gaba da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, tare da tilastawa mutane barin gidajensu.

Hakan na ƙara jefa manoma da makiyaya cikin tsaka mai wuya, saboda irin ta'asar da ƴan bindiga ke yi musu.

Gwamnati da hukumomin tsaro na ci gaba da ƙoƙarin dakile ayyukan ƴan bindiga ta hanyar tura jami’an tsaro da kuma ƙara yawan sintiri a yankunan da ake fuskantar hare-hare.

Duk da haka, mazauna yankunan karkara na ci gaba da buƙatar ƙarin kariya daga jami’an tsaro domin su samu damar gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya yi kira ga 'yan Najeriya bayan hirar El Rufa'i

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hare-hare a wasu ƙauyukan jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun farmaki ƙauyukan ne a ƙananan hukumomin Gusau da Bukkuyum inda suka kashe mutum huɗu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng