Bayan Saukar Farashin Abinci, Tinubu Ya Yi Magana kan Tallafin Man Fetur

Bayan Saukar Farashin Abinci, Tinubu Ya Yi Magana kan Tallafin Man Fetur

  • A ranar Talata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci taron majalisar APC a Abuja a fadar shugaban kasa.
  • A yayin taron, Tinubu ya yi magana kan tallafin mai, inda ya ce matakan da gwamnati ke dauka suna karfafa tattali
  • Shugaban kasar ya bayyana cewa an inganta harkokin tsaro, kuma ana kokarin tallafa wa matasan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci taron majalisar APC da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa.

Rahotanni sun nuna cewa taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar da kuma mukarraban gwamnati.

Tinubu
Tinubu ya yi jawabi a taron APC a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya wallafa bidiyon jawabin da Bola Tinubu ya yi a wajen taron a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron, shugaban kasar ya bayyana cewa Najeriya na kan turbar ci gaba, yana mai cewa matakan da gwamnatin sa ke dauka suna kara bunkasa tattalin arziki.

Bola Tinubu ya jaddada muhimmancin hada kai domin gina kasa, tare da yin kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da hakuri da manufofin gwamnati.

Tinubu ya halarci taron majalisar APC

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar jam’iyyar APC da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa a Abuja.

A yayin taron, Tinubu ya jaddada cewa Najeriya na kan turbar ci gaba, yana mai cewa gwamnati na daukar matakan da za su inganta rayuwar ‘yan kasa.

Ya bayyana cewa kodayake wasu daga cikin manufofin gwamnati sun kasance masu wahala, amma hakan yana da muhimmanci wajen kawo ci gaba mai dorewa.

Maganar cire tallafin man fetur

Shugaban kasa ya ce cire tallafin man fetur yana daya daga cikin muhimman matakan da gwamnatin sa ta dauka domin ceto tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC

"Ba yadda Najeriya za ta tsira idan har aka ci gaba da biyan tallafin fetur. A yau, ina alfahari da cewa kudin da jihohi ke samu daga gwamnatin tarayya sun ninka sau uku,"

- Bola Tinubu

Ya kara da cewa ana kokarin samar da hanyoyin tallafa wa kananan hukumomi, tare da bunkasa harkokin ilimi ta hanyar asusun NELFund domin bai wa matasa damar samun ilimi mai nagarta.

Tinubu
Tinubu da manyan APC a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Harkokin tsaro sun inganta inji Tinubu

Tinubu ya jaddada cewa ana samun ci gaba a fannin tsaro, inda ya bayyana cewa al’umma a yankunan da suka daɗe suna fuskantar barazanar tsaro sun fara samun sauki.

Shugaba Bola Tinubu ya ce mutanen wurare kamar Birnin Gwari sun fara komawa noma cikin kwanciyar hankali.

"Ina farin cikin cewa daya daga cikin manyan kalubalen da muke fuskanta na tsaro yana ingantuwa. Jama’a na komawa gonaki, kuma suna cin moriyar noman da suke yi,"

Kara karanta wannan

Tinubu zai sauke Ganduje a shugaban APC? Sakataren jam'iyya ya magantu

- Bola Tinubu

Shugaban ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai wajen gina kasar, yana mai cewa abin da ke faruwa a duniya yana koyar da mu muhimmancin bunkasa kasashenmu.

APC ta yi magana kan makomar Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta musanta cewa za ta sauke Abdullahi Ganduje daga shugabancin da yake rike da shi.

Sakataren jam'iyyar ne ya bayyana haka bayan wani taro da suka gabatar a fadar shugaban kasa kan makomar APC a ranar Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng