IBB: 'Dalilan Kitsa Harin Rashin Imani da Ya Kashe Tsohon Shugaban Kasa, Murtala'

IBB: 'Dalilan Kitsa Harin Rashin Imani da Ya Kashe Tsohon Shugaban Kasa, Murtala'

  • Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana wasu muhimman batutuwa a kan kisan tsohon shugaban kasa, Janar Muhammad Ramat
  • An kashe tsohon shugaban ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Fabarairu na shekarar 1976, inda aka yi wa motar da yake ciki ruwan alburusai
  • Janar IBB mai ritaya ya tabbatar da cewa an fara shirin kashe shugaban ne tun daga lokacin da ya karɓi mulkin kasa a shekarar 1975

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaJanar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya ce makircin da ya kai ga kisan tsohon shugaban kasa, Janar Murtala Ramat Muhammed, a ranar 13 ga Fabrairu, 1976, ya fara ne tun daga lokacin da ya karɓi mulki a shekarar 1975.

Kara karanta wannan

Littafin IBB: Fitaccen Lauya, Falana zai maka Janar Babangida a kotu, ya jero dalilai

Wannan na kunshe a cikin littafin da tsohon shugaban kasa, Janar IBB ya wallafa, wanda ya bayyana tarihin rayuwarsa da kuma wasu muhimman abubuwa da suka faru a lokacin mulkin soja.

Ramat
Janar IBB ya fadi wanda suka kashe Manjo Janar Murtala Muhammed Hoto: @Searchmediamx/Universal history archive
Asali: Getty Images

A cewar jaridar Vanguard, IBB ya bayyana cewa an fara fakon Janar Murtala Muhammed ne saboda yaki amincewa da raba mulki tsakaninsa da wasu manyan sojoji uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dalilin kisan Janar Murtala Muhammad," IBB

Imran Muhammad ya wallafa a shafinsa na X cewa, bayan juyin mulkin da ya kifar da Janar Yakubu Gowon, IBB ya ce Murtala Muhammed ya yi watsi da tsammanin matasan sojoji.

Ya bayyana yadda Murtala Muhammed ya samu goyon bayan ‘yan Najeriya saboda wasu shahararrun matakan da ya ɗauka na inganta rayuwarsu.

Sai dai, ya nuna nadama kan yadda har yanzu ƙasar ba ta farfaɗo daga matakin da ya ɗauka na sallamar manyan ma’aikatan gwamnati a shekarar 1975 ba.

Yadda aka so Murtala ya gudanar da mulki

Kara karanta wannan

Martanin jiga jigan siyasar Najeriya kan abin da littafin IBB ke kunshe da shi

IBB ya ce a lokacin da aka yanke shawarar cewa Murtala Muhammad Ramat ya zama shugaban kasa, an yi fatan zai raba karfin ikon mulki dai–dai da takwarorinsa.

Wannan kuwa ya shafi yadda zai tafiyar da mulki tare da sauran manyan hafsoshin soja biyu, watau Brigediya Olusegun Obasanjo da Brigediya Theophilus Danjuma.

Ya bayyana cewa:

"Mun san halayen Muhammed da kyau, mun kuma san cewa sai an kai ruwa rana sosai kafin ya amince da irin wannan tsarin."
"Don haka, yayin da sauran matasan manyan hafsoshi suka tsaya a wani ɗaki, Kanal Wushishi, Laftanar-Kanalo Joe Garba, Abdullahi Mohammed da Shehu Musa Yar’Adua suka tafi tare da Brigediya Muhammed, Obasanjo da Danjuma zuwa wani ɗaki don tattauna yadda za a yi tsarin mulki na haɗin gwiwa, inda Murtala zai raba iko da sauran shugabanni biyu."

Ramat ya kori manyan sojoji

IBB ya bayyana cewa Murtala Muhammed ya ƙi amincewa da wannan tsari gaba ɗaya, kuma ya ɗauki matakai masu tsauri kwana ɗaya bayan wannan taron.

Kara karanta wannan

An bankado umarnin Tinubu da zai illata Arewa, NARTO ta gargadi gwamnati

Ramat
Janar IBB ya fitar da dalilan kashe shugaban kasa Hoto: @Searchmediamx
Asali: Twitter

A cewarsa:

"Taron ya ɗauki sa’o’i da yawa har zuwa tsakar dare. A ƙarshe, Murtala Muhammed ya amince da zama shugaban ƙasa, amma ya nace cewa ba zai zama ƙarƙashin kowa ba!"
"Bayan kammala taron, a cikin salon mulkinsa mai tsauri, ya yi gaggawar sanar da ritayar manyan hafsoshi washegari, tare da naɗa sababbin shugabanni.
Duk wani soja da ke da mukamin Janar ko wanda ya fi wani daga cikin sababbin shugabanni girma, an tilasta masa yin ritaya.

Ya bayyana cewa ya bi wannan mataki da maye gurbin wadanda ya kora da sababbin sojoji, tare da bin kadun duk wasu jami'an gwamnatin Gowon da aka samu da tara kudin haram.

Yadda aka kashe Janar Murtala

Janar IBB ya bayyana cewa an gudanar da yunkurin juyin mulki a ranar Juma'a, 13 ga Fabrairu, 1976, wanda Laftanal Kanal Bukar Suka Dimka ya jagoranta.

Ya ce:

"Shirin masu juyin mulki shi ne su kitsa kwanton bauna a kan hanyoyin kusoshin gwamnati na zuwa aiki a safiyar waccan rana. "

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulmai ta taso IBB a gaba, ta ce abin kunya ne wasu magangunan da ya yi a littafinsa

"Bisa ga binciken da aka yi daga baya, Manjo Ibrahim Rabo, Kyaftin Malaki Parwang, da Laftanar William Seri, ƙarƙashin jagorancin Laftanar-Kanal Bukar Suka Dimka, sun shirya don su tare ayarin Murtala Muhammed."
"Dimka ya raba wa kowane ɗan tawagarsa takamaiman aikin da zai yi. A yayin harbin Murtala, an ce Laftanar Seri ya yi rashin imani, har ya ƙona fiye da casbi guda ɗaya na harsasai a cikin motar da ke dauke da shugaban ƙasa."

An yi wa Osinbajo gyara a kan batun IBB

A wani labarin, mun wallafa cewa fadar shugaban kasa ta musanta kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na cewa IBB ya azabtar da Bola Tinubu.

A jawabin da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida na daga cikin wadanda suka ba Tinubu kwarin gwiwar fadawa siyasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel