El Rufai Ya Fadi Shirin Gwamnatin Tinubu da Zai Jefa Manoma cikin Talauci
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana ra'ayinsa kan manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Nasir El-Rufai ya bayyana cewa wasu daga cikin manufofin da shugaban ƙasan yake aiwatarwa ba su dace ba ko kaɗan
- 'Dan siyasar ya soki shirin shigo da abinci daga ƙasashen waje, ya ce hakan hanyar lalata harkar noman cikin gida ne
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yi tsokaci kan wasu daga cikin manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa duk da yana goyon bayan wasu daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu, tsarin da ake bi wajen aiwatar da su ba daidai ba ne.

Asali: Facebook
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Arise TV a makon yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufai ya soki manufofin Tinubu
Nasir El-Rufa’i ya kuma soki wasu daga cikin manufofin gwamnatin, musamman a ɓangaren noma.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya yi gargaɗin cewa shigo da abinci daga ƙasashen waje ba zai magance hauhawar farashin kaya ba, sai dai zai jefa manoma cikin fatara kuma ya lalata harkar noma a cikin gida.
"Ba na son na yi hukunci ko na yi wata magana kan gwamnati saboda duk abin da zan faɗa za a iya fassara shi a matsayin suka."
“Ina goyon bayan wasu daga cikin manufofin. Yawancin manufofin tattalin arziƙin suna da kyau, amma tsarin aiwatar da su ba daidai ba ne."
"Bugu da ƙari, mutanen da aka ba su ragamar aiwatar da waɗannan sauye-sauyen ba su da ingancin da ake buƙata."
“Kuma ina ganin wasu daga cikin waɗannan sauye-sauyen ba su dace ba. Ba za ka iya magance matsalar tashin farashin kayan abinci ta hanyar lalata harkar noma a cikin gida wajen shigo da abinci daga ƙasashen waje ba."
"Ko da farashin abinci zai ragu, amma manoma za su shiga cikin fatara saboda ana tilasta musu yin gogayya da kayayyakin noma da aka sanya musu tallafi daga Turai da wasu ƙasashe.”
"Ina da matsala da da dama daga cikin waɗannan manufofi, kuma ina tattaunawa da wasu manyan jami’an gwamnati, inda nake ba su shawarwari a sirrance. Amma bana son na wuce iyakar hakan."
- Nasir Ahmed El-Rufai
Jam'iyyar APC ta caccaki El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi wa Nasir Ahmed El-Rufai martani kan sukar shugaba Bola Tinubu da Nuhu Ribadu.
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Ijeoma Arodiogbu, ya yi wa El-Rufai tatas kan kalaman da ya yi a kan manyan mutanen guda biyu.
Arodiogbu ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna, har yanzu yana jin haushi ne saboda ya gaza cimma buƙatunsa na son zuciya da ya nema a gwamnatin Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng