An Shiga Tashin Hankali a Bauchi, Ango da Yayar Amarya Sun Rasu Mintuna 30 kafin Ɗaura Aure

An Shiga Tashin Hankali a Bauchi, Ango da Yayar Amarya Sun Rasu Mintuna 30 kafin Ɗaura Aure

  • Ango da yayar amarya sun rasu a wani mummunan hatsarin mota ana saura ƴan mintuna ɗaura aure a garin Boto da ke jihar Bauchi
  • Shaidu sun ce hatsarin ya faru ne a lokacin da angon da yayar amaryar ke hanyar zuwa wurin da aka shirya bikin a yankin Tafawa Balewa
  • Wani ɗan uwan ango ya ce lamarin ya gigita mutanen Bato musamman amarya wacce ke cike da ƙunci a ranar da aka shirya ɗaura mata aure

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Wani mummunan hatsarin mota mai matukar tayar da hankali ya rikita al’umma a garin Boto da ke karamar hukumar Tafawa Balewa, a jihar Bauchi

Hatsarin motar ya yi ajalin wani sabon ango mai suna Abba Musa, da yayar amarya Maryam Suleiman, ana saura mintuna 30 kacal kafin daurin aure.

Kara karanta wannan

Soyayya ta ƙare: Wani ɗan Najeriya ya lakaɗawa budurwarsa dukan tsiya har ta mutu

Taswirar Bauchi.
Ango da yayar amarya sun mutu ana saura mintuna 30 ɗaura aure a Bauchi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rahotan da Leadership ta tattara ya tabbatar da cewa hatsarin ya faru ne yayin da angon da yayar amarya ke hanya daga Murno zuwa wurin bikin da aka shirya a Boto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan iftila'i ya girgiza al'ummar kauyen Bato musamman ƴan uwa da abokan arziki, waɗanda suka taru domin shaida auren da za a ɗaura na ƴan uwansu.

Yadda ango da yayar amarya suka rasu

Wani ganau ya bayyana cewa lamarin ya gigita al’ummar yankin, a yanzu mutane da dama sun shiga firgici da alhinin abin da ya faru.

Saminu Boto, dan uwan ango, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa wannan babban rashi ne da ya durkusar da duka iyalai biyu.

Ya ce:

“Wannan babban rashi ne da ba za a iya mantawa da shi ba, ba mu yi tsammanin haka ba, duk mutanen garin Boto sun shiga yanayin alhini.”

Ya ce gidan amarya, wanda ya kamata ya kasance cikin shiri da farin ciki, ya koma wani wuri na kuka da jimamin wannan rashi.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankar ƙauna: Allah ya yi wa mahaifi da kawun ɗan takarar gwamna rasuwa

An yi jana'izar mamatan a Bauchi

Saminu ya bayyana marigayi ango, Abba Musa a matsayin matashi mai kyakkyawar zuciya da burin gina rayuwa mai kyau da matarsa, Raihanatu Suleiman.

Ya ƙara da cewa yayar amarya, Maryam Suleiman, an santa da goyon bayan iyalinta, kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙulla soyayyar ango da amarya.

Rahotanni sun nuna cewa bayan faruwar hatsarin, an yi jana’izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wane hali amarya ke ciki?

A halin yanzu, an ce amarya Raihanatu Suleiman na cikin baƙin ciki mara misaltuwa na rashin angon da ake dab da ɗaura masu aure da yayarta a ranar da ya kamata ta zama ta farin ciki.

Mutane da dama a garin Boto da kewaye sun bayyana wannan rana a matsayin rana mafi muni da suka taba gani a tarihin yankin.

Budurwa ta rasu sanadiyyar dukan saurayi

A wani labarin, kun ji cewa wani matashi ɗan soyayya ya lakaɗawa budurwarsa dukan kawo wuƙa har rai ya yi halinsa a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Rundunar ƴan sandan Legas ta cafke wanda ake zargin kuma za ta gurfanar da shi a gaban kotu da zaran an kammala bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262