"Mun Inganta Tsaro," Shugaba Tinubu Ya Yi Magana bayan El Rufai Ya Faɗi Maganganu
- Yayin da ake ta surutu kan kalaman Malam Nasiru El-Rufai, Bola Tinubu ya maida hankali kan lamarin tsaron al'ummar Najeriya
- Da yake buɗe taron ƴan sanda a Ogun, shugaban ƙasa ya ce gwamnatinsa ta inganta hukumomin tsaro ta hanyar samar masu da kayan aiki
- Mai girma Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa jami'an tsaro domin magance dukkan ƙalubalen tsaron ƙasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta karfafa ayyukan hukumomin tsaro don shawo kan kalubalen da ke fuskantar kasar.
Bola Tinubu yi yi wannan bayani ne a lokacin da yake bude taron koli da shakatawa na manyan jami’an ‘yan sanda karo na biyar (CARSPO) a Abeokuta, jihar Ogun.

Asali: Twitter
Tinubu, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya jaddada cewa tsaro yana da matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki, Vanguard ta kawo.

Kara karanta wannan
"Dole Tinubu ya samu nasara da ƙarfin ikon Allah," Minista ya hango abin da zai faru a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce gwamnatinsa na samar da kayan aiki ga jami'an tsaro da nufin tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin tsaro da kuma yaki da aikata laifuka.
Tinubu ya roƙi a ba ƴan sanda haɗin kai
Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai da ‘yan sanda don inganta tsaro a cikin al’umma, yana mai cewa:
"Ko da kuwa an bai wa ‘yan sanda kudade da kayan aiki, ba za su samu nasara ba idan ba tare da hadin kan al’umma ba. Hadin kai da goyon bayan jama’a na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro."
Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar da aniyar gwamnati na karfafa ayyukan ‘yan sanda ta hanyar samar da kyakkyawan yanayi da kayayyakin aiki ga jami'ai.
Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba ƙarafafa rundunar ƴan sanda ta hanyar gyara barikin ‘yan sanda, samar da motocin aiki da kayan kare kai da na yaki da miyagun laifuka

Kara karanta wannan
Ministan tsaro ya yi albashir ga Arewa kan matsalar ta'addanci, ya tabo alaka da Nijar
Inganta jin dadin ma’aikata da ‘yan sanda
Tinubu ya kara jaddada cewa sabon mafi karancin albashi da gwamnati ke kokarin aiwatarwa yana daga cikin matakan da aka dauka don kara jin dadin ma’aikata da jami’an tsaro.
Ya ce gwamnati tarayya za ta ci gaba da ba da tallafi da kwarin gwiwa ga jami’an tsaro domin su yi aiki tukuru wajen kare kasa da al’ummar da ke cikinta.
Mai girma Tinubu ya ce gwamnatinsa ta bullo da sababbin matakan farfado da tattalin arziki da nufin jawo hankalin masu zuba jari, rage hauhawar farashi, da kuma daidaita yanayin tattalin arziki.
Gwamnatin Tinubu ta shigo da motoci
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sayo motocim noma daga ƙasashen ketare a ƙoƙarin inganta harkokin noma da bunkasa tattalin arziki.
Hakan na ɗaya daga cikin mataka da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka domin magance ƙarancin abinci da ake fama da shi a ƙasar nan da samar da hanyoyin neman arziki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng